Bashir Gurgu: Tsohon mabaracin da ke koyar da matasa sana'a

Bashir
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A wajen wasu masu mutanen, nakasa ko kuma buƙata ta musamman hanya ce ta samun damar fara yawon barace-barace, wanda ya fara al'ada ga wasu ta mayar da nakasar wata hanya ta samun kuɗi cikin sauƙi ba tare da shan wahala ba.

Amma shi Malam Bashir Abdullahi gurgu, a wajensa bara ƙasƙantacciyar sana'a ce, wadda ke kashe zuciya, wanda hakan ya sa ya zaɓi zama cikin hayaƙi da zafin wutar walda domin samun abin sakawa a bakin salati, maimakon yawo yana roƙon mutane kafin ya samu na abinci.

A cikin unguwar Kawo da ke birnin Kaduna, sunan Bashir Gurgu mai walda fitaccen suna ne, wanda mutane ke zuwa daga wurare masu nisa domin kawo masa aiki, wanda a cewarsa wataƙila saboda mutane sun ga yadda ya jajirce ne wajen dogaro da kansa da kuma ƙoƙarin taimkon wasu matasa.

A wajensa, "bara ba sana'a ba ce," saboda haka ne kuma ya zaɓi koyon sana'ar walda a cibiyar koyar da nakasassasu sana'a a Abuja, sannan ya koma Kaduna domin yaƙi da barace-barace.

A kullum shagon Bashir na cike da mutane - mas kawo aiki da masu koyon aiki - waɗanda ya ce su ne suke ƙara masa ƙarfin gwiwar cigaba da abin da ya saka a gaba ba tar da gajiyawa ba.

Rayuwa a Abuja

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallon bidiyon

Malam Bashir Abdullahi haifaffen jihar Kaduna ne, amma daga bisani ya koma babban birnin tarayya Abuja domin rayuwa da neman abin sakawa a bakin salati domin ciyar da iyali.

Sai dai nakasa da rashin aiki takamaime sun sa Bashir ya tsinci kansa a cikin masu yawon barace-barace a titunan Abuja, wanda a cewarsa a farko ya fara jin daɗi domin yana samun kuɗi sosai, da har ya fara tunanin ita ce hanya mafi sauƙi da zai yi amfani da ita domin riƙe kansa da iyalinsa.

Sai dai bayan wani lokaci sai Malam Bashir ya fara fahimtar cewa barace-baracen nan ba ta dace da shi ba, wanda hakan ya sa ya fara neman hanyar da yake ganin za ta ɓille masa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Ba da lalurar aka haife ni ba, amma na samu labarin cewa ina ƙarami ne na kamu da rashin lafiya, har ta kai na zama haka," in ji Bashir wanda ya ce yanzu shekarunsa za su haura 45 zuwa 50.

Ya ce yana cikin yawon bara a Abuja ne a zamanin da Nasir El-Rufai yake minista aka tsince su, aka tura su cibiyoyin nakasassu domin koyar da masu buƙata ta musamman sana'o'i domin a shirin gwamnati na yaƙi da barace-barace.

"Da na je sai na zaɓi in koyi walda, inda na shekara biyu har na koy kuma na ƙware," in ji a lokacin da yake kunna wutar walda.

Bayan ya kammala samun horon ne Bashir ya zaɓi ya koma jihar Kaduna inda ya ci gaba da sana'ar walda. Amma maimakon waldar kaɗai domin ya riƙa samun ƴan kuɗaɗensa, sai ya zama mai horar da wasu domin zama abin koyi ga ɗaruruwan matasa.

"Ina koyar da matasa – lafiyayyu da masu buƙata ta musamman. Yanzu haka wasu sun buɗe nasu wuraren sana'ar suna aikinsu, har wasu ma sun fara koyar da su," in ji shi.

Abin alfaharina

Walda

Malam Bashir Gurgu ya ce yana koyar da matasa san'ar ce ba tare da neman ko sisi ba, saboda a cewarsa, "wannan wata gudunmuwa ce da mutum za iya bayarwa domin rage zaman banza, da rage yawon barace-barace, wanda kuma hakan zai rage yawaitar ayyukan assha."

Ya bayyana cewa yadda rayuwarsa ta canja daga mutum mai yawon barace-barace zuwa mai dogaro da kansa na cikin manyan abubuwan da ya fi alfahari da su, "idan na tuna cewa na daina bara, nakan ji daɗi.

"Yanzu an kawo lokacin mutane lafiyyyu da masu buƙta ta musamman na zuwa neman taimako a wajena," in ji shi.

Ya kuma buƙaci sauran masu buƙata ta musamman da su "daina dogara da bara," domin a cewarsa ba sana'a ba ce, sannan ya yi kira gare su da su je su koyi sana'a su fara dogaro da kan su.

Yunƙurin yaƙi da bara

Duk da cewa Bashir yana da shago babba a unguwar Kawo, inda yake sana'arsa har kuma yake koyar da wasu, ya ce babban abin da yake ci masa tuwo a ƙwarya shi ne ganin har yanzu akwai ɗimbin mabarata a titunan jihar Kaduna da ma wasu jihohin ƙasar.

"Ba na jin daɗi idan na ga mutane suna yawon bara. Bara ba sana'a ba ce mai kyau. Amma wasu ba da son ransu suke bara ba, babu yadda za su yi ne kawai. Wannan ne ya sa nake jin zafi idan na ga mabarat na ƙara yawa, kuma babu yadda zan yi."

Ya ce idan ya samu dama, zai buɗe cibiyoyin horar da masu buƙata ta musamman sana'o'in hannu domin, "idan suka fara jin daɗin dogaro da kai, duk za su daina yawon barace-barace."

Ya ce yana kira ga gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su shigo su haɗa ƙarfi da ƙarfe, domin ya cika burinsa "na yaƙi da yawon bara."

"Kamar yadda gwamnati ta horar da ni sana'a, nima ina so in horar da wasu saboda gwmnati ita kaɗai ba za ta iya ba. Wannan ne gudunmuwar da za mu iya bayarwa."

Koyon walda wajen Bashir

Walda

Ko da BBC ta je shagon Malam Bashir Gurgu, ta same shi ne yana wasu aikace-aikace, amma ba waldar ba saboda rashin wutar lantarki a lokacin, kuma injinsa na walda ya lalace.

Amma a can bayan layin da yake, akwai wani matashi wanda ya samu horo daga wajen Bashir, har ya ƙware ya samu kuɗi ya buɗe nasa shagon, wanda ya ce yakan je wajen ya yi aiki idan babu wuta.

Shehu Umar da Lawal Ya'u matasa ne lafiyayyu da muka samu a shagon, kuma suna cikin manyan waɗanda suke koyon sana'a a wajen Bashir Gurgu.

"Na koyi sana'ar walda a wajen Oga Lawal duk da yana da buƙata ta musamman, amma yanzu a sanadiyarsa ina da aikin da nake dogaro da shi domin har na buɗe nawa shagon," in ji Lawal.

Shi ma Shehu ya ce an kai shi wajen Malam Bashir ne ya koya sana'ar walda, kuma ya koya, ya ƙware, kuma ya buɗe shago har ya fara shiry-shiryen ɗaukar wasu ya koya musu.

"Wannan kaɗai abin alfahari ne a wajena," in ji Bashir.

A ƙarshe, Bashir ya ce, "zan dage wajen karatun yarana na boko da na addini domin ina fata yarana su girma su zama abin alfahari a Najeriya. Da yardar Allah za su zama manyan mutane masu daraja."