Martinez da Cubarsi sun buga wa Barcelona wasa na 50 kowanne

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Masu tsaron bayan Baarcelona, Inigo Martinez da Pau Cubarsí sun buga wa ƙungiyar wasa 50 kowanne ranar Asabar.

A ranar ce Barcelona ta kai zagayen ƴan 16 a Copa del Rey, bayan da ta doke Barbastro 4-0.

A wasan ne Barcelona ta fara amfani da Szczęsny da kuma Toni Fernández a karon farko, yayin da Martinez da Cubarsí kowanne ya yi karawa ta 50 a ƙungiyar.

An fara wasan na ranar Asabar da Martinez daga baya aka sauya shi a minti na 62, inda Cubarsi ya shiga madadinsa.

Cubarsi ya fara yi wa Barcelona tamaula a Janairun 2024 a karawar Copa del Rey da Unionistas.

Shi kuwa Martinez ya koma Baarcelona tun kan fara kakar 2023, wanda ya fara yi mata wasa cikin watan Satumbar 2023 a gasar La Liga da Osasuna.

A kakar bana ya yi karawa 26, inda Barcelona ke fatan ƴan wasan za su zama fitattu a nan gaba a duniya.