Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An amince wa sojojin Rasha su adana maniyinsu kafin zuwa fagen daga
Sojojin Rasha da ke yaƙi a Ukraine zasu iya ajiye daskararren maniyinsu a na'uarar ajiya maniyyi kyauta, a cewar wani babban lauyan ƙasar.
Shugaban ƙungiyar lauyoyin Rasha Igor Trunov ya sanar da kamfanin dillancin labarai na Tass , cewar Ma'aikatar Lafiya ta bayar da amsa ga kiransa da na ajiye maniyin sojojin kuyata, da sauyi kan tsarin Inshorar lafiya na tilasa.
Rasha ta kira dakaru da basa yaƙi har 300, 000, bayan koma baya da aka samu a yakin da ake a Ukraine, inda wasu daga cikinsu suka fara ziyartar asibiti don a dasakarar da maniyinsu a cewar rahoton.
Mr Trunov ya fitar da wata sanarwa a shafin Twitter, ya ce ƙungiyar sa a madadin ma'aurata, musamman wadan da aka tura mazajensu yaƙi, a mastayin dakaru na musamman don yaki da Rasha.
Sai dai ma'aikatar lafiya bata kai ga cewa komai bakan kalaman na Mr Trunov. Amma lauyan ya fadawa Tass cewar " yanke hukucin kan yiwuwar samar da tallafin kuɗi daga kasafin kudin gwamantin tarayya, don ajiya kwayoyin halitta da ke cikin maniyyi, ga 'yan ƙasar da aka nemi su shiga cikin dakaru na musamman na 2022-2024".
Rasha ta fara mamaye Ukraine a wata Fabareru da dakarun soji 200,000. Ba wai ta rasa fiye da rabin inda ta mamaye tun a farkon yakin ba, amma ta rasa dubun dabatar abubuwa. masu yawa.
A watan Satumba Shugaban Vladimir Putin ya sanar da "kiran wadan da zasu shiga cikin rudunar ta musamman don yaƙar Ukraine, kuma adadin wadan suka jikkata na ci gaba da ƙaruwa. Sama da dakarun Rasha 250,000 da ya kamata su shiga yaƙin ne suka tsere don kaucewa shiga rundunar sojin ta musssamnan.
Kwanaki kadan zuwa raanr da za a fara kiran dakarun, shafin yanar gizo na birni n abiyu mafi hirama a St Petersburg Fontanka, ya rawaito gwammon maza na tururwar zuwa IVf da asibitoncin ajiye maniyin, don a daskarar musu da maniyyi da cike bayanai don baiwa matansu damar amfani da shi.
Andrei Ivanov da ga asibitin Mariinsky dake birnin, ya ce maza na shirye-shiryen shiga cikin rundunar ta musamman, da wadan ke da shirin barin Rasha.
Ba kasafai maza da mata 'yan Rasha ke zuwa asabitin ba " ko wata ƙila," za a yi kuskure, Fontanka ta ce, kuma ba su taɓa tunanin daskararwa ko daukar bayanai bincike ba a baya.
Ko da yake, wannan mafita na nufin ko da mutum zai mutu, ko ya de na haihuwa, zai iya amfani da daskararen wajen samun 'ya'ya.