Mbappe ya lashe ƙyautar Mahou Cinco saboda rawar da ya taka a Disamba

Kylian Mbapppe

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kylian Mbappe shi ne ya lashe ƙyautar Mahou Cinco Estrellas a matakin fitatcen ɗan wasa a watan Disamba.

Ɗan ƙwallon tawagar Faransa ya buga wa Real Madrid wasa shida a cikin watan karshen shekarar 2024.

Daga ciki ya zura ƙwallo biyar a raga a karawar La Liga uku da Champions League da kuma Fifa Club World Cup da ya yi.

Ranar 18 ga watan Disamba Real Madrid ta lashe Intercontinental Cup, bayan doke Pachura 3-0 a karawar karshe, kuma Mbappe ya ci ƙwallo ɗaya daga ciki.

Cikin wasa shida da Mbappe ya yi wa Real a Disamba, bai samu cin ƙwallo ba a La Liga da Athletic Bilbao ta yi nasara 2-1 ranar Laraba 4 ga watan Disambar 2024.

Mbappe ya koma Real Madrid daga Paris St German kan fara kakar bana a matakin wanda yarjejeniyarsa ta kare a ƙungiyar ta Faransa.

Yanzu dai Real Madrid ta mayar da hankali kan Copa del Rey da Spanish Super Cup, wanda take fatan yin abin kirki a kakar nan.

Bayan nan tana fatan sake lashe La Liga da kuma Champions League a 2024/25.

Ƙwallayen da Mbappe ya ci a cikin watan Disambar 2024

La Liga Liga Lahadi 1ga watan Disamba

  • Real Madrid 2 - 0 Getafe (Ya zura ɗaya a raga)

La Liga Asabar 7 ga watan Disamba

  • Girona 0 - 3 Real Madrid (Ya zura ɗaya a raga)

Champions League Talata 10 ga watan Disamba

  • Atalanta 2 - 3 Real Madrid (Ya zura ɗaya a raga)

FIFA Club World Cup Laraba 18 ga watan Disamba

  • Real Madrid 3 - 0 Pachuca (Ya zura ɗaya a raga)

La Liga Lahadi 22 ga watan Disamba

  • Real Madrid 4 - 2 Sevilla (Ya zura ɗaya a raga)