Lewandowski ne kan gaba a cin ƙwallaye a La Liga

Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Barcelona, Robert Lewandowski shi ne kan gaba a cin ƙwallaye a La Liga kawo yanzu mai 20 a raga, bayan kammala wasannin mako na 24.

Ranar Litinin Barcelona ta koma matakin farko a teburin La Liga, bayan da ta yi nasara a kan Rayo Vallecano da cin 1-0.

Kuma Lewandowski ne ya ci ƙwallon a bugun daga kai sai mai tsaron raga a wasan da ya ja hankalin masu bibiyar tamaula.

Cikin ƙwallo 65 da Barcelona ta ci a kakar nan a La Liga, Lewandowski yana da 20 a raga, wanda ya zura 33 a dukkan karawa a ƙungiyar.

Sau ɗaya ɗan wasan ya ci ƙwallo uku rigis a La Liga a kakar nan, shi ne wanda Barcelona ta je ta doke Alaves 3-0 ranar Lahadi 6 ga watan Oktoban 2024.

Kylian Mbappe ne na biyu mai taka leda a Real Madrid mai 17 a raga, sai Raphinha mai 17 mai taka leda a Barcelona.

Barcelona mai maki 51 iri ɗaya da na Real Madrid ta koma jan ragamar teburin La Liga ranar Litinin, bayan cin ƙwallo 65 aka zura mata 25 a raga.

Ita kuwa Real Madrid, wadda ta koma matsayi na biyun teburi an zura mata ƙwallo 23 ta ci 52, bayan kammala wasannin mako na 24.

Atletico Madrid ce ta ukun teburi da maki 50, wadda ta ci ƙwallo 39 aka zura mata 16.

Jerin ƴan wasan da ke kan gaba a cin ƙwallaye a La Liga:

  • Lewandowski Barcelona 20
  • Mbappé Real Madrid 17
  • Raphinha Barcelona 13
  • Budimir Osasuna 13
  • Sancet Athletic Club 12
  • García Deportivo Alaves 10
  • Lukébakio Sevilla 10
  • Pérez Villarreal 10
  • Sørloth Atletico Madrid 9
  • Júnior Real Madrid 8