West Ham za ta bai wa Lyon aron Benrahma

An wallafa

West Ham ta amince za ta bayar da aron Said Benrahma, domin buga wasanni zuwa karshen kakar bana.

Idan har sun cimma matsaya, ana sa ran sayar da dan kwallon mai shekara 28 kan fam miliyan 15 cikin kunshin yarjejeniyar, idan ya taka rawar-gani

Benrahma ya koma West Ham daga Brentford a Oktoban 2020, inda yarjejeniyarsa za ta karkare a karshen kakar 2026.

To sai dai ɗan kwallon ba ya kan ganiya a kaka uku da ya yi a West Ham.

Ya buga Europa League a bara a wasan karshe da Fiorentina da cin kwallon farko a bugun fenariti da West Ham ta tashi 2-1.

Daga nan Benrahma ya kasa cin kwallo a wasa 22 da ya buga a bana, an kuma ba shi jan kati a FA Cup a karawar da Bristol City ta yi nasara ranar 16 ga watan Janairu.

Haka kuma tawagar Aljeriya ba ta gayyaci ɗan kwallon ba zuwa gasar cin kofin Afirka da ake yi a Ivory Coast.

Haka kuma kungiyar ta West Ham United ba ta sallama tayin da Real Betis ta yi wa ɗan kasar Sifaniya, Pablo Fornals ba.

Sai dai a shirye take ta bar ɗan wasan ya koma Sifaniya, amma tana son a yi mata tayi mai tsoka a kanshi bayan ya buga wasa hudu a Premier League a kakar nan.