'Babu abin da zai saukar da farashin dala a Najeriya'

An wallafa

Tashin da farashin dala ya yi wani abu ne da ba za a iya kauce masa ba a Najeriya, saboda matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin Najeriya.

Daga watan Janairun 2022 da ake sayar da dala kan naira 565, zuwa wannan watan na Oktoba naira ta rasa darajarta da kashi 28, kamar yadda shafin Nairametrics’ FX da ke bibiyar darajar kudi ya bayyana.

A cikin abin da ya gaza kwanaki 10, farashin dala ya karu da kusan naira 54, biyo bayan sanarwar da babban bankin kasar CBN ya fitar na sauya fasalin kudin kasar.

A ranar Talata a Abuja an fara sayar da dala kan naira 839, ko da yake wasu jihohin irinsu Kano farashin bai kai haka ba dalar ba ta fi 818 ba.

Da dama daga cikin masu sana'ar canji za ka tarar da shagunansu babu kowa ciki, sun zauna babu abin yi, kamar yadda Mustapha Zakariya wani mai kamfanin musayar kudi na BDC ya bayyana.

"Da yawanmu mun daina zuwa kasuwa saboda bamu da abunyi, mafi yawanmu mun fi samun dalar ne ta CBN da ake kira (beading) kuma yanzu an fi shekara rabon da a ba mu" in ji shi.

'Yan canji na tsaka mai wuya'

Mafi yawan abokan hulda yanzu ba sa kai dalarsu domin a ba su naira, a cewar Malam Mustapha. Suma ajiyarta suke yi domin duk kwana guda dalar daraja take karawa kamar yadda darajar naira ke zibewa.

"A baya akwai wasu hanyoyi da ke rage wahalhalun samun dala da su, kamar tallafin da bankuna ke bai wa matafiya neman lafiya ko ilimi ko kuma kasuwanci, amma yanzu babu ko daya da ake samu.

"Amma idan kana da wani makusanci za ka iya samun adadin da kake so na dubu hudu da ake bayar wa a hukumance." a cewar Mustapha.

A baya akan samun dala daga bankunan kasuwanci da CBN da kuma masu kai wa kasuwa su sayer domin samun naira, amma bincike ya nuna a yanzu babu ko daya cikin wadan nan da ke aiki.

Mustapha ya ce bukatar da ake da ita ta dala yasa "ko dubu 20,000 kake nema sai dai ka hada ta da dubu daya dubu biyu domin kuwa samun dala a dunkule ya zama tarihi a Najeriya".

Ya shaida wa BBC cewa idan kana da asusu na banki na kudaden ketare zai zama kana da kudi a ciki, amma ba za ka iya cire kudin ba a lokacin da kake so.

Idan wani abokin huldarka ya yi maka aiken kuaddaen ketare daga bankin kamar "GT" zuwa "First Bank" ba zai zo ba domin babu dalar a bankunan.

"Duk tashin da dala ke yi 'yan canji ake zargi, babu mai bai wa 'yan canji dala a hukumance, kuma babu wanda ya san tayaya suke samun dalar, balle kuma ba sa samu yanzu. "Muna cikin tsaka mai wuya. Ta bangaren gwamnati ba mu samu abin da muke so ba, ta bangaren mutane kuma zarginsu na kara yawaita a kanmu," in ji Mustapha.

'Matakin da bankuna suke dauka"

Masana na cewa ba kowa ne ke jin dadin wannan tashin da farashin dala ke yi ba, ko da bankunan kasuwanci da suke hada-hadar kudi a fadin Najeriya, domin lamarin na shafar ayyukansu.

A don haka bankunan sun dauki matakai da suke gani za su iya saukaka faduwar da naira ke yi a kasar, ta hanyar bayar da kananan kudaden kasashen ketare.

Idan mutum na da asusun ajiya na kudaden ketare da ake kira (domiciliary) za ka iya ajiye kudinka ciki ko nawa ne, kuma a baya za ka iya cire ko nawa kake so a ko wanne lokaci, sai dai lamarin ya sha ban-ban a yanzu.

Abokan hulda na zuwa da shirin cire kudi kamar dala 100 ko sama da haka, amma bankuna sai su kare da basu dala mai 10 ko 20 ko 5 a wasu lokutan, a dabararsu zai rage tsadar da ake fara da ita.

A wasu lokutan sai dai su bayar da katin ATM, to amma a ina ne za ka iya amfani da ATM domin cire kudaden a cikin Najeriya?

Ga tsarin tallafin BTA da PTA da sauransu, yanzu bankunan kasuwanci a fadin Najeriya sun daina ba yar da dala a hannu (cash) sai da kati idan an fita waje a cire. Sai dai masana na cewa tsarin cike yake da magudi da kuma cuwa-cuwa.

'Dala daya za ta iya kai wa naira 1,000 nan da Disamba'

Ba wani abu bane ya janyo tashin dala a fadin Najeriya ba illa daina bai wa gwamnati kudi da kamfanin mai na NNPC ya yi kwata-kwata. Ta hanyarsa ne gwamnati ke samun dala mai yawa.

Man fetur shi ne "babban abin da Najeriya take sayerwa ta samu dala, kuma yanzu NNPC ya yi wata takwas zuwa tara bai bayar da komi ba" in ji Dakta Muhammad Shamsuddeen na jami'ar Bayero da ke Kano.

Hakan ya biyo bayan ikirarin da NNPC ke yi na biyan kudaden tallafi (subsidy), wanda tun daga nan aka fara fuskantar karancin dalar a hukumance.

"Hakan ya sa ita kanta gwamnati idan tana bukatar dala sai dai ta bayar da takardun lamuni da ake kira (Eurobond) ta samu kudaden.

"Dalili na baya-bayan nan shi ne, sauya fasalin kudi da CBN ya sanar da cewa zai yi a kwanakin baya, abin da zai faru shi ne mutane za su fito da kudadensu su sayi kudaden waje.

"Wannan ya kara bukatar da ake da ita na dalar, wanda ita ba a da bukatar yin wata doka a kanta a Najeriya." in ji Dr Shamsuddeen.

Ya yi zargin mutanen da suke yawan zuwa bankuna suna karbar BTA da PTA domin samun riba, tunda akwai banbancin farashi tsakanin farashin gwamnati da na kasuwa.

Duk wadannan abubuwa su ne ba za su bar dala ta zauna wuri daya ba, akwai bukatarta da yawa akwai kuma karancinta a kasuwa.

"Muna fargabar daga nan zuwa watan Disamba dala za ta iya kai wa naira 1,000.

"Da barar da bankuna ke yi na bayar da dala kanana babu inda za ta kai Najeriya sai baya, domin kananan kadara babu abin da suke yi sai ta'azzara lamura," in ji Dr.

'Da halin da ake ciki babu abin da zai tsayar da farashin dala a Najeriya'