Abin da ya faru a gidan yarin da aka kai wa hari a Ukraine

.

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Da safiyar ranar 29 ga watan Yuli ne aka kashe fiye da fursunonin Ukraine 50 a wani hari da aka kai a wani gidan yari da ake kira Prison Camp 120 a Turancin Ingilishi da yake wani yanki da Rasha ta mamaye.

Ukraine da Rasha na zargin juna da kai harin. Ƙwararrun masu bicike sun faɗa wa BBC abin da ya sa ba su gamsu da bayanin da Rasha ta yi ba.

Gargaɗi: Wannan maƙala na ɗauke da bayanai masu tayar da hankali.

Abin da aka gani a sashen ajiya na gidan yarin ya sosa rai.

Hotuna sun nuna an yasar da gawarwakin mutanen da suka ƙone. A waje akwai ƙarin gawarwaki baje a ƙasa.

Kimanin fursunonin yaƙi 50 na Ukraine aka kashe wasu 73 suka samu rauni a wani hari da ya grgiza ƙasar kuma ya tunzura mutane yin zanga-zanga a Ukraine da ƙasashen waje.

An yi kashe-kashen a yankin Donetsk da ke iƙirarin samun ƴancin kai.

Olenivka, ƙauye mafi kusa, ya kasance ƙarƙashin ikon ƴan tawaye masu samun goyon bayan Rasha tun bayan da faɗa ya ɓarke a gabashin ƙasar a 2014.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan tantance hotunan da suka fito daga ɓangaren Rasha, mun yi magana da ƙwararru kan makamai da masu bincike na kimiyya, a wani yunkuri na gano abin da ya faru da kuma abin da ba a sani ba game da harin a gidan yarin Prison 120.

Mun kuma tattauna da tsofaffin fursunoi da aka saki ƴan makonni kafin kai harin kuma waɗanda suka yi bayani dalla-dalla kan halin da suka shiga kafin kai harin.

Ma'aikatar tsaron Rasha ba ta ce komai ba game da buƙatarmu ta neman ta mayar da martani.

An fara buɗe gidan yarin da a hukumance aka fi sani da Volnovakha da ake killace mutane - a nesanta su da jama'a cikin shekarar 1999.

A yanzu ana amfani da shi don tsare dubban fursunoni - daga farar-hula da ƴan sa-kai zuwa mayaƙan Ukraine - waɗanda dukkansu mayaƙa masu samun goyon bayan Rasha suka kama a yankin Donetsk da Kudancin Ukraine.

Amma cikin fursunonin akwai ɗaruruan mayaƙa daga rundunar Azov. An sauyawa rundunar ƴan sa-kai da aka kafa a 2014 fasali inda aka shigar da ita cikin ƴan sintirin Ukraine.

Bayan shafe tsawon lokaci suna bai wa birnin Mariupol, mai tashar jirgin ruwa kariya, a farkon wannan shekarar abin da ya samar da tsaro a katafaren kamfanin sarrafa ƙarafa na Azovstal, 'yan sintirin sun yi fice a matsayin ɗaya daga cikin manyan mayaƙan Ukraine.

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yadda aka lalata kamfanin sarrafa ƙafa na Azovstal

A cewar jami'an Ukraine da kuma jerin sunayen mutanen da lamarin ya shafa da Rasha ta fitar, akwai alamun akasarin waɗanda aka kashe ko suka jikkata sun fito ne daga rundunar soji ta Azov.

Da take sanar da faruwar lamarin a Olenivka, sjojin Rasha sun zargi Ukraine da kai harin inda ta ce a kai harin ne ta hanyar amfani da na'urar roka ta Amurka da ake kira Himars.

"Duk wata aika-aika da aka tafka kan al'ummar Ukraine, laifin Zelensky ne [Shugaban Ukraine], da gwamnatinsa da Amurka da ke mara musu baya," kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Rasha, Laftanar Janar Igor Konashenkov ya faɗa a gidan talabijin ɗin ƙasar.

Jami'an Rasha sun nuna wasu ɓaraguzon na'urar ta Himars da ake zargin an gano daga wajen da aka kai harin.

Denis Pushilin, shugaban ƴan a-waren ƙungiyar DPR da ke samun goyon bayan Rasha, ya yi ikirarin dakarun Ukraine sun kashe musu sojoji domin ɓoye laifukan yaƙin da aka tafka.

Musamman, hare-hare kan farar hula da Pushilin ya yi ikirarin Zelensky ne ya ba da umarnin kai shi.

"Bayanan da wasu fursunoni suka yi hujja ne," kamar yadda Pushilin ya faɗa wa gidan Talabijin na Rasha. "Kyiv ta yanke shawararta lalata shi."

Wani hoto da aka ɗauka ta sararin samaniya a ranar bayan fashewar ya nuna yadda wani gini ya ruguje.

Tsofaffin mutanen da aka tsare a gidan gyaran halin sun ce ginin yana wani yankin masana'antu da ke da nisa daga babban barikin da suke zama.

BBC ta tuntuɓi wasu ƙwararru kan makamai da masana kimiyya domin yin nazari kan hujjojin da ake da su - hotunan da aka ɗauka daga sararin samaniya da bidiyon ginin da aka kai wa harin - domin gano shawarar Rasha cewa Ukraine ce ta kai harin da makaman atilari.

Sakamakon bincikensu ya yi kamanceceniya.

"Babu yadda za a yi a ce makamin roka ne ya ruguza ginin, in ji Bob Seddon, tsohon babban jami'in fasaha na harsashi na sojojin Birtaniya.

Irin ɓarnar da aka gani a hotunan, a cewarsa, babban al'amari ne. Amfani da na'urorin Himars zai haifar da gagarumar ɓarna.

Sannan a cikin ginin, gawarwakin da aka gani a hotunan da kafafen yaɗa labaran Rasha suka fitar, ba su sauya kamanninsu ba, in ji Dr Shehan Hettiaratchy, babban mai aikin fiɗa kuma babban jami'in kula da masu damuwa a Kwalejin Imperial da ke London.

Sai dai da alamun an ƙona gawarwakin kamar yadda wata likita ƴar Birtaniya, Dr Saleyha Ahsan, da ke da ƙwarewa sosai a yankunan da ke fama da rikici.

Ƙarancin hujjojin da ake da su, wani malami, Pete Nortom da ake aiki a sashen fasahar abin fashewa da tsaro a makarantar koyar da harkokin tsaro ta Burtaniya da ke Shrivenham ya ce an dasa wani abin fashewa da aka inganta da mai.

Game da maƙasudin amfani da irin wannan na'urar, shafin intanet na CAT-UXO da ya mayar da hankali wajen wayar da kai kan abubuan fashewa ya ce "ana iya amfani da irin na'urar wajen ta da wuta ko lalata wata hujja da binciken masana kimiyya."

Wata hujja ɗaya da aka samu mai cike da taƙaddama da muka kasa tabbatar da sahihancinta ita ce kiran waya, da ake zargi jami'an leƙen asiri na Ukraine sun ƙwace.

Ƴan sa'oi bayan da Rasha ta zargi Ukraine da kai harin, Ukraine ta saki abin da kiran wayar da aka naɗa ya ƙunsa.

A ciki, wasu mutum biyu da ba a san ko su wanene ba suna tattaunawa kan yadda aka kwashe jami'an Azov zuwa wani ɗakin ajiyar kayayaki da aka killace kwanaki biyu kafin kai harin.

Ɗaya daga cikin mutanen ya ce an harba makaman Rasha masu linzami domin rufe ƙarar fashewar a ɗakin ajiyar kayan kuma wataƙila sun dasa abin fashewar ne tun kain kai harin."

Da BBC ta bukaci karin bayani, hukumomin Ukraine sun ki cewa uffan.

Ganin cewa ba mu samu damar shiga wurin da aikata laifukan ba, yana da matukar wahala a fadi hakikanin abin da ya faru a wurin a daren.

.

Asalin hoton, Reuters