Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Henderson ya koma Al-Ettifaq ta Saudi Arabia
Kyaftin din Liverpool, Jordan Henderson ya koma Al-Ettifaq mai buga babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia.
Dan kwallon tawagar Ingila, mai shekara 33 ya amince da kunshin yarjejeniyar fam miliyan 12 har da karin tsarabe-tsarabe.
A sakon ban kwana da ya yi wa Liverpool, ya ce zai bar kungiyar inda ya yi kaka 12, wadda ya lashe Premier League da Champions League a ita da sauran nasarori.
Henderson yana Liverpool tun bayan da ya koma Anfield daga Sunderlandn kan fam miliyan 20 a watan Yunin 2011.
Ya buga karawa 492 da cin kwallo 33 da bayar da 57 aka zura a raga ya kuma dauki kofi bakwai a Liverpool.
Henderson zai yi aiki a karkashin Steven Gerrard, wanda shine kociyan Al-Ettifaq.
Mutanen biyu sun taka leda tare a Liverpool daga baya Gerrard ya bar Anfield a 2015.
Henderson ya zama kyaftin din Liverpool a 2015, wanda ya ja ragama ta lashe Champions League a 2019 daga baya ta dauki Uefa Super Cup da Fifa Club World Cup a kakar gaba.
Haka kuma Al-Ittihad ta taya wani dan wasan Liverpool, Fabinho kan fam miliyan 40 ranar 14 ga watan Yuli.