Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Ban san cewa shan barasa saboda nishaɗi zai iya yi min illa ina matashiya ba’
- Marubuci, Hazel Martin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Panorama
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Ina da shekara 31 da haihuwa likitoci suka shaida mun cewa zan mutu idan har ban daina shan barasa ba.
Abin ya ɗaure min kai saboda ba kullum ne nake sha ba, ba na shan barasa ni kaɗai kuma ina sha ne ba don komai ba illa don nishaɗi, ba don na kasance ƴar giya ba.
Amma idan aka yi nazarin yadda nake shan barasa tun da na kai shekara 20 da haihuwa, za a iya ɗaukar sa a matsayin mai yawa. Ban ɗauke shi a matsayin wani abu daban ba saboda mutanen da ke kewaye da ni su ma haka suke yi - amma yanzu lamarin ya zame tashin hankali a gare ni.
Ba da daɗewa ba bayan na haihu, na ziyarci likita domin ina fama da kasala a kodayaushe. Don haka aka yi min gwajin jini da kuma na ƙarfin huhu.
Da aka zurfafa bincike sai aka ga na kamu da ciwon hanta sakamakon barasar da na ke kwankwaɗa.
Na koma gida daga asibitin a gigice, ina ɗauke da ɗiyata. Yana yiwuwa hakan ya faru da ni amma bai kamata a ce ni kaɗai ba ne.
Na buƙaci sanin abin da hakan ke nufi kan yadda ake shan barasa a Birtaniya, sai na fara bincike kan shirin 'Panorama' na BBC.
Adadin mace-mace sakamakon ta'ammali da barasa ya yi tashin gwauron zabi a Birtaniya a shekarun baya bayan nan.
A duniya baki ɗaya, wani rahoton hukumar lafiya ta duniya da aka fitar a watan yuni-wanda ya yi nazarin alƙaluma daga shekarar 2019- ya gano cewa ana samun mace-mace da suka kai miliyan 2.6 da za a iya alaƙantawa da shan barasa a kowace shekara,
Yayin da matsalar ta fi yawa tsakannin maza - musamman masu shekaru da yawa - ana samun ƙaruwa a adadin mata ƴan ƙasa da shekara 45 da ke mutuwa sakamakon cututtukan hanta da za a iya alaƙantawa da shan barasa, a cewar ofishin ƙididdiga na Birtaniya a nazarin da ya yi tsakanin shekarun 2001 zuwa 2022.
Idan muka sha barasa da yawa a lokaci guda - misali cikin dare ɗaya - za ta fi yi mana illa kan a ce mun sha irin wannan adadin amma cikin wani tsawon lokaci.
Bincike na baya bayan nan, da wata tawagar haɗin gwiwa ta jami'o'in Landan da na Oxford da Cambridge da ke Birtaniya ta gudanar ya nuna cewa kwankwaɗar barasa a zama guda na iya yin illa kusan nunki huɗu kan lafiyar hantar ɗan'adam.
Idan muka yi tunanin ɗirkar barasa a zama guda, abin da ke fara zuwa tunanin mu shi ne mutane shin sha sun yi tilis suna kwance a bakin hanya ko kuma a gidajen giya. Amma a zahrin gaskiya, shan barasan da ke iya yin illa ba sai ya kai wannan matakin ba.
A Birtaniya, kwankwaɗar barasa a zama guda na iya zama shan kofi shida zuwa sama na barasa a zama ɗaya ga mata, ko kuma kofi takwas zuwa sama ga maza.
A asibitin koyarwa ta Kings College da ke Landan, likitar hanta Debbie Shawcross ta shaida mun cewa tana kula da mata masu shekaru 40 zuwa 50 a kai a kai waɗanda da ke fama da cutar hanta.
Ta ce: “Sun kasance mata ma'aikata, kuma wataƙila suna da iyalai ,” in ji ta. "Ba 'yan giya ba ne ... amma suna shan barasa da yawa a matsayin nishaɗi."
Ban cika shekara 40 ba tukuna, amma halin da nake ciki ya yi kama da waɗanda ta ke sifantawa.
Lokacin da nake matashiya, zan iya shan fiye da abin da aka ayyana a matsayin shan barasa da ya wuce misali a dare ɗaya. Ban yi tunanin akwai wata illa a tattare da hakan ba har sai da aka gano cutar da na ke fama da ita.
Bayan gwaje-gwajen jinin da aka yi min an tura ni Asibitin New Victoria na Glasgow, inda aka ɗauki hoton cikina, kuma a karshe aka yi mun gwajin da ake kira 'fibroscan'. Kuma duk waɗannan sun faru ne cikin kusan shekara guda.
'Fibroscan' wani nau'i ne na ɗaukar hoton ciki wanda ke auna ƙarfin hanta. Idan aka samu maki bakwai a kan ma'aunin KPA (naúrar da ake amfani da ita don auna matakin iskar oxygen a cikin jini) ko ƙasa da haka ana ɗaukar sa a matsayin daidai. Amma nawa ya kai matakin10.2.
Wannan na nuni da cewa akwai matsala da hantata - wanda idan ba don an gano ba, kuma da ban daina shan barasa ba, da na kamu da mummunan ciwon hanta.
Na karɓi sakamakon gwaje-gwajen asibitin da aka yi min ne a watan Fabrairun 2024. Likita na, Dr Shouren Datta ya ce idan har na ƙaurace wa barasa akwai yiwuwar samun sauƙi daga matsalar da ta addabi hantata.
Ba ƙaramin sa'a na ci ba da aka gano matsalar da sauri, domin in yi yunkurin ɗaukar mataki a kai.
Likitoci sun gano matsalar ce a lokacin da ake bin diddigin kasalar da na ke fama da ita.
Amma ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke tattare da ciwon hanta ita ce daga farko ba ta bayyana wasu alamu.
Mutane bakwai cikin 10 masu fama da ciwon hanta ba su san komai game da shi ba har sai an kwantar da su a asibiti bayan alamunta sun fara bayyana.
Abin da ya faru ke nan da Emma Jones, mai shekaru 39, ƴar asalin arewacin Wales. Na haɗu da ita watanni 15 bayan an yi ma ta dashen hanta.
Kamar ni, Emma ta kasance mai shan barasa domin nishaɗi, inda ta ke ma'ikaciya kuma mai kyakkyawar rayuwar zamantakewa. Amma yayin da ake shiga kullen cutar korona abubuwa suka fara taɓarɓare mata - a mafi munin lokaci, inda ta kasance tana shan kwalaben barasa uku a rana.
An kwantar da Emma a asibiti inda ta gano tana fama da ciwon hanta da ya kai mummunan mataki. An ce da wuya ta rayu fiye da sa'o'i 36.
Amma ta taki sa'a, ta farfaɗo - bayan ta cika watanni shida ba tare da ta sha barasa ba - ta sam aka yi mata dashen da take matuƙar buƙata.
Har yanzu Emma na kan murmurewa amma yanayin rayuwarta ya mutukar sauyawa. Za ta kasance tana shan magunguna har ƙarshen rayuwarta kuma garkuwar jikinta na da matuƙar rauni, ma'ana yana da wahala jikinta ya iya yaƙar ƙwayoyin cuta.
Amma tana da rai kuma tana da lafiya, kuma ta ce tana da kwanciyar hankalin da ba ta taɓa samu ba. Na samu ƙwarin gwiwa daga yanayin rayuwarta.
Adadin mata masu shan barasa
A cewar alƙaluman baya bayan nan daga ma'aikatar ƙididdiga ta Birtaniya, daga shekarar 2018, ciwon hanta ya kasance cikin cututtuka uku da ke kan gaba wurin janyo mace-mace tsakanin mata da ke da shekara 39 zuwa 45 kowance shekara.
''Adadin mata masu shan barasa ya ruɓanya cikin ƙanƙanin lokaci...kamar shekara 10,'' In ji Prof Fiona Measham, ƙwararriya a fannin bincike kan ta'ammali da barasa da miyagun ƙwayoyi a Jami'ar Liverpool.
Binciken da ta gudanar ya nuna cewa a shekarun 1990 da 2000, masana'antar barasa ta Birtaniya ta karkata akalarta ne kan mata mashayan barasa, inda aka ɓullo masu da abubuwan sha da ke ɗauke da barasa kamarsu 'alcopops' - kuma aka yi amfani da al'amura kamar su ƴancin mata domin tallata masu barasar.
Tana tunanin waɗannan matakan sun ƙara haɓɓaka halayyar shan barasa a tsakanin mata matasa, wanda hakan ke yin matuƙar tasiri kan al'umma baki ɗaya.
''Abin da muke gani yanzu shi ne shan barasa ya ragu a tsakanin matasa, amma ba a samu wani sauyi ba tsakanin waɗanda suka kai shekara 30 zuwa 50 ba,'' in ji ta
Muna ci gaba da ganin wannan mummunan tsarin a yau a masana'antar barasa, in ji Farfesa Carol Emslie, daga Jami'ar Glasgow Caledonian. Sai dai kawai a yanzu ana zuzuta abubuwa ne kamar su ''prosecco'' da "gin o'clock" da "wine time" a matsayin hanyar da mata za su shaƙata su kuma kula da kansu bayan sun kammala aikin ranar.
Portman group, wadda ke wakiltar masana'antar barasa, ta ce:
Duk da yake "ƙaruwar kamuwa da cutar hanta da ke da alaƙa da barasa tsakanin mata da maza a Birtaniya babban abin damuwa ne, yana da muhimmanci a tuna cewa barasa ta kasance abin da doka ta amnice da ita."
Sun ce ƙa'idojinta… "ba su bayar da kariya daga tallace-tallace da ke da alaƙa da jinsi ba " amma yana daidaita "mafi ƙanƙantar ma'auni don masu sarrafa barasa wurin tallata kayansu cikin aminci".
Kuma yana "yunƙurin ci gaba da…(sa) bunƙasa shan barasa da kima tare da kuma tabbatar da cewa masana'antar ta yi abin da ya dace a kodayaushe ."
Watanni da dama bayan na karɓi sakamakon gwaje-gwajen asibiti, na sake komawa domin a yi min gwajin 'Fibroscan' domin ganin ko abubuwa sun sauya.
Na samu kwanciyar hankali da na ga cewa na sauko daga ma'aunin 10.2 zuwa 4.7 - na sake dawowa matakin da ake bukata.
Na yi mamakin irin sauyin da na samu bayan na daina shan barasa, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
Ba na da niyyar sake komawa shan barasa - An shawarce ni da kar in yi tunanin komawa,
Na shafe kusan shekara guda ban sha ko ɗigo ɗaya ba, kuma ina jin dadin jikina - amma har yanzu nakan ɗan yi kewar ta a yanayin da ba zan iya kwatantawa ba.
Barasa ta kasance wani da ya samo asali a al'adar mutanen Birtaniya. Muna shan barasa a bukukuwan ranar haihuwa da bukukuwan aure da jana'iza. Sannan kuma babu shakka akwai lokacin bukukuwa, wanda ke somawa kafin Kirsimeti kuma ya ci gaba har zuwa ranar Sabuwar Shekara.
A lokacin da na ke tasowa, an mayar da barasa kamar jiki kuma ban yi la'akari da irin matsin lambar da ake fuskanta na shan barasa ba har sai da aka tilasta mun barin ta.
Kaurace wa barasa ba abu ne mai sauki ba. An ɗauki lokaci mai tsawo kafin na saba da rashin bukatar barasa a yanayi daban-daban ba.
Ina ganin wannan wani ɓangare ne da ya zame matsala a gare ni a lokacin, kuma ya kasance matsala ga al'ummarmu a yanzu.