Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City na nazarin ɗaukar Frimpong, Barcelona na zawarcin Omorodion
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya an nazarin miƙa tayi kan ɗan wasan bayan Bayer Leverkusen da Netherlands Jeremie Frimpong, mai shekara 23 tare da abokin wasansa na ƙasar Holland ɗin Sepp van den Berg mai shekara 22, wanda ya koma Brentford daga Liverpool a bazarar da ta gabata. (Football Transfers)
Barcelona ta ayyana ɗan wasan gaba na Sifaniya Samu Omorodion mai shekara 20 a matsayin wanda zai maye gurbin ɗan wasan Poland Robert Lewandowski mai shekara 36. (El Nacional)
Mai wakiltan ɗan wasan gaban Canada Jonathan David ya shaidawa ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan da suka haɗa da Juventus da Inter Milan da Liverpool da Manchester United cewa ɗan wasan zai buƙaci kwantiragin Fam milayan 5 kowanne shekra kafin ya fara tunanin barin Lille a matsayin kyauta idan kwantiraginbsa ya ƙare a bazara mai zuwa.(Tuttosport)
Arsenal da Liverpool na cikin jerin ƙungiyoyin Turai da ke zawarcin ɗan wasan tsakiya na Eintracht Frankfurt da Sweden Hugo Larsson, mai shekara 20. (Teamtalk)
Chelsea da Newcastle da Crystal Palace na nazarin mika tayi kan dan wasan baya na Benfica da Portugal Tomas Araujo mai shekra 20. (O Jogo)
Manchester United ta fara tunanin yadda za a yi ta dawo da ɗan wasan baya Alvaro Carreras, mai sahekara 21, wanda ta saida wa Benfica a bazara. (Marca)
Liverpool ta bayyana sha'awarta kan ɗan wasan Sweden Daniel Svensson, mai shekara 22, yayin da Manchester United da Arsenal suka fara tunanin ɗaukar ɗan wasan daga ƙungiyar Nordsjælland.
Real Madrid ta fara sanya ido kan ƴan wasan baya da suka haɗa da ɗan wasan baya na Al-Nassr da Sifaniya Aymeric Laporte, mai shekara 30, da ɗan wasan Tottenham Pedro Porro, mai shekara 25. (Relevo)
Tsohon ɗan wasan Italiya Vincenzo Montella shi ne kan gaba a cikin jerin ƴan takarar da ke neman zama kocin AS Roma kuma da alama zai iya karya kwantiraginsa da hukumar ƙawallon ƙafa na Turkiyya. (Gazzetta dello Sport)