Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An sauya ranar wasan Real Madrid da Athletic a La Liga
Mahukuntan gasar La Liga sun sanar da rana da lokacin da za a fafata a wasannin mako na 16 da na 19 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Hakan ya sa aka dawo da karawar mako na 19 kusa-kusan nan da ya kamata a kece raini tsakanin Athletic Club da Real Madrid.
Kenan filin wasa na San Mammes zai karɓi bakuncin fafatawar Athletic da Real Madrid ranar Laraba 4 ga watan Disamba.
A kuma makon ne Real Madrid za ta je gidan Girona a Montilivi a karawar mako na 16 a La Liga ranar Asabar 7 ga watan Disamba.
An yi wannan sauye-sayen ne saboda gasar Spanish Cup da ake fafatawa tsakanin wadda ta lashe La Liga da ta biyu a gasar da wadda ta ɗauki Copa del Rey da ta biyu.
Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki shida tsakani da Barcelona, wadda ke jan ragama, bayan wasan mako na 13, Real tana da kwantan wasa ɗaya.
Real Madrid za ta je gidan Laganes a karawar mako na 14 a La Liga ranar Lahadi 24 ga watan Nuwamba.
Daga nan Liverpool za ta karɓi bakuncin Real Madrid a Champions League ranar Laraba 27 ga watan Nuwambar.