Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Kuskuren binciken ICPC kan bashin karatu da ziyarar Tinubu a Katsina
Wannan maƙala ce da ke kawo muku bitar muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata
Mun yi kuskure a sanarwar bincikenmu kan bashin karatu - ICPC
A cikin makon nan ne hukumar ICPC mai yaƙi da almundahana a Najeriya ta ce ta yi kuskure a sanarwar da ta fitar kan binciken kuɗaɗen bashin karatu na NELFUND.
Tun da farko cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Alhamis ta nuna cewa daga cikin naira biliyan 100 da aka fitar domin bai wa ɗaliban ƙasar bashin karatu, fiye da naira biliyan 71 sun yi ɓatan dabo.
To sai dai a zantawarsa da BBC, shugaban hukumar, Barista Musa Adamu Aliyu ya ce kuskure aka samu wajen fitar da sanarwar.
Ya ce binciken da hukumarsa ke yi, tana yi ne kan jami'o'in da ake zargi ba sa bai wa ɗaliban kuɗaɗen da aka tura musu, ba zargi kan hukumar NELFULD ba.
''Haƙiƙanin gaskiya babu wasu kuɗi da ake zargin cewa an yi kwana da su na bashin karatu, muna magana ne a kan kuɗin da aka tura wa makarantu,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Gwamnonin arewa maso gabas sun gudanar da taro a Damaturu
A cikin mako ne kuma ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya suka gudanar da taro a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Gwamnonin sun jaddada ƙudirin aiki tare domin magance matsalolin da ke addabar yankin.
Ƙungiyar gwamnonin ta yi kira ga rundunar sojin Najeriya, da sauran hukumomin tsaro da shugabannin al'umma domin sake shirin tunkarar matsalar tsaro musamman a yankin.
Taron na zuwa a yayin da yankin ke fama da sabbin hare-haren daga mayaƙan Boko Haram da na ISWAP.
Gobara ta tashi a barikin sojoji na Maiduguri
Haka ma a tsakiyar makon ne hedikwatar rundunar haɗin gwiwa da ke yaƙi da Boko Haram ta a Maiduguri ta sanar da tashin gobara a barikin soji na 'Giwa barracks' da ke birnin Maiduguri, lamarin da ya yi sanadiyar ƙonewar rumbun makamai na barikin.
Gobarar ta janyo fashewar abubuwa tare da haddasa fargaba a tsakanin al'umma a Maiduguri saboda ƙara mai ƙarfin gaske da aka ji a ƙwaryar birnin da kewaye.
Mazauna birnin Maiduguri sun shiga zullumi sakamakon tashin gobarar, inda galibin jama'a suka zaci cewa 'yan Boko Haram ne suka kai hari.
'Masu garkuwa sun kashe limami da ƴaƴansa a Zamfara'
A dai makon mai ƙarewa ne aka samu labarin kisan gillar da wasu ƴanbindiga suka yi wa babban limamin Maru a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, Alƙali Salihu Suleiman, da ƴaƴasa uku.
Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta bayyana lamarin a matsayin "wani mummunan matsayi" da matsalar garkuwa da mutane ta kai a Najeriya.
Cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar a Najeriya, Isa Sanusi ya ce limamin mai shekara 79 da ƴaƴansa uku sun shiga hannun ƴanbindiga ne a lokacin azumin watan Ramadana a watan Maris kuma sun kashe su ne duk da karɓar kuɗin fansa naira miliyan 11 cikin miliyan 20 da suka buƙata.
Amnesty ta bayyana cewa waɗanda lamarin ya shafa sun fuskanci "matsananciyar azaba" a hannun ƴanbindigan.
'Maƙiya na neman shiga tsakanina da Tinubu'
Gwamnan jihar Kebbi Dakta Nasir Idris, ya zargi waɗanda ya kira ''masu son ɓata tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu'' da ƙirƙirar labarin cewa zai bar jam'iyar APC.
Gwamnan dai na mayar da martani ne ga wani rahoto da ke waɗari a shafukan sada zumunta, cewa shi da wasu gwamnonin APC huɗu na shirin ficewa daga jam'iyyar, tare da janye goyon bayansu ga Shugaba Tinubu.
A taron da ya kira na 'yan jam'iyyar APC a jihar Kebbi a cikin makon mai ƙarewa domin ƙaryata labarin, Gwamnan ya ce ana zargin ya koma SDP kuma mutane ne da ba sa son zaman lafiya ke yada wannan jita-jita.
Ya ce shi bai ga dalilin barin APC ba, kawai maƙiyansa na siyasa ke son shiga tsakaninsu da Bola Tinubu ganin cewa akwai kusanci da alaƙa mai kyau tsakaninsu.
Gwamnan ya jaddada cewa yanzu ya soma goyon-bayan shugaban kasa da jam'iyyarsa don haka duk masu yaɗa wannan raɗe-raɗin za su yi su gama.
Tinubu ya yi ziyarar aiki ta kwana biyu a Katsina
Haka kuma a ranar Juma'ar makone ne, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa jihar Katsina da ke arewacin ƙasar domin ziyarar aiki ta kwana bbiyu.
Gwamnan Katsina Dikko Radda, da tsohon Gwamna Bello Masari na cikin manyan mutanen da suka tarɓe shi tun daga filin jirgi.
Jim kaɗan bayan isarsa ne kuma ya yi wa rundunar sojin ƙasar jawabi.
Shugaban ya kuma ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta yi.