Abin da kuke son sani kan Fifa Club World Cup 2023

An wallafa

Kawo yanzu an san kungiyoyi shidan da za su fafata a FIFA Club World Cup da za a gudanar a cikin watan Disambar 2023.

Ranar Asabar Fluminense ta cike gurbin karshe na shida, bayan da ta yi nasara a kan Boca Juniors ta lashe Copa Libertadores a Rio de Janeiro.

Manchester City ce za ta wakilci nahiyar Turai, wadda za ta fara gasar daga matakin daf da karshe da za a yi gumurzu a Saudi Arabia.

Jadawalin wasannin Fifa Club World Cup:

Man City za ta kara da ko dai Club Leon ko Urawa Red Diamonds ranar 19 ga watan Disamba.

Fluminense za ta kece raini da Al Ahly ko Al-Ittihad ko kuma Auckland City.

Wadanda suka ci karawar daf da karshe za su hadu a wasan karshe ranar 22 ga watan Disamba.

Kungiyoyin da suke cikin Fifa Club World Cup 2023:

Al Ahly (Masar) - Wadda ta lashe kofin zakarun Afirka CAF Champions League 2023.

Al-Ittihad (Saudi Arabia) - Mai masaukin baki, wadda ta lashe gasar Saudi Arabia kakar 2022/23.

Auckland City (New Zealand) - Wadda ta lashe kofin zakarun Oceania a 2023.

Fluminense (Brazil) - Wadda ta dauki Copa Libertadores a 2023.

Leon (Mexico) - Wadda ta dauki CONCACAF 2023.

Manchester City (Ingila) - Wadda ta dauki Champions League a 2023.

Urawa Red Diamonds (Japan) - Wadda ta lashe kofin zakarun Asia a 2023.

Wasannin da za a buga a Fifa Club World Cup a Saudi Arabia:

Zagayen farko:

Al-Ittihad da Auckland City ranar 12 ga watan Disamba a King Abdullah Sports City, Jeddah

Zagaye na biyu:

Leon da Urawa Red Diamonds ranar 15 ga watan Disamba a Prince Abdullah Al Faisal Stadium, Jeddah

Al Ahly da Al-Ittihad ko kuma Auckland City ranar 15 ga watan Disamba a King Abdullah Sports City, Jeddah

Wasan daf da karshe:

Fluminense da Al Ahly ko kuma Al-Ittihad ko kuma Auckland City ranar 18 ga watan Disamba a King Abdullah Sports City, Jeddah

Manchester City da Leon ko kuma Urawa Red Diamonds ranar 19 ga watan Disamba a King Abdullah Sports City, Jeddah

Wasan neman mataki na uku:

Ranar 22 ga watan Disamba a Prince Abdullah Al Faisal Stadium, Jeddah

Wasan karshe:

Ranar 22 ga watan Disamba a King Abdullah Sports City, Jeddah