Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City za ta ziyarci Burnley, Chelsea da Liverpool a jadawalin Firimiya
Zakarun gasar Premier na 2022/2023 za su fara kare kambinsu a kakar wasa ta bana ranar Juma'a 11 ga watan Agusta.
Man city za ta fara wasan farko a wannan kaka ne da karawa da zakarun Championship wato Burnley da tsohon ɗan wasan Man City Vincent Kompany ke jagoranta.
Luton Town za ta fara wasanta na farko a Premier tun shekarar 1992, da karawa tsakaninta da Brighton ranar asabar 12 ga watan na Agusta, a daidai lokacin da Sheffield United za ta karɓi baƙuncin Crystal Palace.
Arsenal wadda ta zo ta biyu a gasar da ta wuce za ta fara wasannin bana da karawa da Nottingham Forest.
Mauricio Pochettino zai fara jagorantar Chelsea a wasan premier na farko da karawa da Liverpool ranar Lahadi 13 ga watan na Agusta.
Shi kuwa sabon kocin Tottenham Ange Postecoglou zai ziyarci Brentford a wasansa na farko.
Manchester United kuwa za ta fara karawar farkon ne da karɓar baƙuncin Wolves a Old Trafford ranar Litinin 14 ga watan na Agusta.
Manchester City, wadda ke murnar lashe kofuna uku a bana, bayan da ta lashe kofin Premier da na FA da kuma na gasar Zakarun Turai, na da burin zama ƙungiya ta farko a Ingila da za ta lashe kofin Premier sau huɗu a jere.
ƙungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta ta ɗauki kofin Premier sau biyar a cikin kaka shida da suka gabata.
Kocin kungiyar Burnley wadda ta lashe kofin Chamopionship a bana, Vincent Kompany ya shafe shekarar 11 yana take leda a Man City, inda ya ci kofin Premier huɗu.
Za a ƙarƙare wasannin kakar 2023/24 ranar Lahadi 19 ga watan Mayun 2024.
Wasannin mako na farko
Juma'a, 11 ga Agusta
Burnley vs Manchester City
Asabar Saturday, 12 ga Agusta
Arsenal vs Nottingham Forest
Bournemouth vs West Ham
Brighton vs Luton Town
Everton vs Fulham
Sheffield United vs Crystal Palace
Newcastle United vs Aston Villa
Lahadi, 13 ga Agusta
Brentford vs Tottenham Hotspur
Chelsea vs Liverpool
Litinin, 14 ga Agusta
Manchester United vs Wolverhampton Wanderers