Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ten Hag ya kara mana kwarin gwiwa a Man United
Raphael Varen ya ce Erik ten Hag ya kara musu kwarin gwiwa kan yadda suke taka leda a kungiyar tun bayan da ya karbi aiki kan fara kakar bana.
Dan kwallon tawagar Faransa ya kara da cewar kociyan ya sa da'a, sannan kowa na kokrin ganin ya bayar da gudunmuwar da kungiyar za ta koma gurbinta.
United na fatan kai wa zagayen ‘yan 16 da zarar ta ci Barcelona a Old Trafford ranar Alhamis – bayan da suka yi 2-2 a makon jiya a Sifaniya.
Varane, mai tsaron baya ya koma taka leda a United a 2018 daga kungiyar Real Madrid.
A kakar ce ta dauki Jadon Sancho daga Borussia Dortmund da kuma Cristiano Ronaldo daga Juventus- duk da haka kungiyar ta kasa kai bante da ta kai an salami Ole Gunners Solsjaer.
Nan da nan aka nada Ralf Rangnick na rikon kwarya – wanda United ta yi ta shida a Premier League a bara.
Dalin da ya sa take buga Europa League a bana, wadda ta kare a ta biyu a wasan rukuni da ya kai take buga karawar shiga 'yan 16 da za su ci gaba da fafatawa.
Daga nan ne United ta dauki Erik ten Hag, wanda yake ta kokarin kai kungiyar kan ganiya – kungiyar ce kadai da ke takarar kofi hudu a Ingila a bana.
Za ta buga wasan karshe da Newcastle a Carabao Cup ranar Lahadi, wadda take FA Cup da Premier da kuma Europa League.
United wadda ta fara kakar bana a gurbin karshe a teburin Premier League, yanzu tana ta uku da tazarar maki uku tsakaninta da Manchester City ta biyu.