Mohamed Deif: Wane ne shugaban sojin Hamas da Isra'ila ke nema ruwa a jallo?

Mohamed Dief

Asalin hoton, Media Sources

Bayanan hoto, Deif ya sha tsallake rijiya da baya na yunƙurin kashe shi a Gaza
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da hari ta saman da ta kai Gaza a makon da ya gabata, da nufin kashe shugaban sashen soji na ƙungiyar Hamas, Mohammed Deif.

Ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce harin -wanda ya faɗa unguwar Al-Mawasi da ke Gaza ya kashe gomman mutane da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato rundunar sojin isra'ila na cewa ''Bayanan da muka samu shi ne mayaƙan Hamas ne kawai ke zaune a sansanin, babu ɗan gudun hijira ko guda''.

Sojojin na Isra'ila sun ce harin ya kashe kwamandan Hamas na yankin Khan Younis, Rafa Salama, wanda ake bayyana shi da ɗaya daga cikin waɗanda suka kitsa harin 7 ga watan Oktoba, kuma makusanci ga Deif.

Haka dai a makon da ya gabatan, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ''babu tabbas ko an kashe Deif a harin''.

Ƙungiyar Hamas ta zargi Isra'ila da yunƙurin “ɓoye yawan mummunan kisan da harin ya yi.”

Gomman shekaru ana nemansa ruwa a jallo

Deif - wanda ke jagorantar Al-Qassam, sashen soji na Hamas - ya shafe gomman shekaru cikin jerin mutanen da Isra'ila ke nema ruwa a jallo, sannan hukumomin Isra'ila sun sha zarginsa da kisan fararen hula da sojoji.

Cikakken sunansa shi ne Mohammed Diab Al-Masry. an haife shi a sansanin 'yan gudun hijira na Khan Younis a 1965.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Deif ya taso a gidan talakawa, inda ya shekafe tsawon lokaci yana sana'ar kaɗi da saƙa tare da mahaifinsa. Daga baya ya yi kiwon kaji a gonarsa kafin ya koma sana'ar tuƙin mota.

Deif na nufin ''Mai ziyara'' ko ''baƙo'', da ke nuni ga rayuwarsa, saboda ya shafe tsawon rayuwar yana sauya wurin zama daga nan zuwa can, domin ɓat da sawu ga Isra'ila.

Ya samu digiri a fannin kimiyya daga Jami'ar Musuluncin da ke Gaza, inda ya karanta darussan physics da chemistry da kuma biology.

A lokacin da yake jami'a ya kasance shugaban kwamitin nishaɗantarwa, inda ya riƙa taka rawa a wasannin daɓe na ban dariya a jami'ar.

A lokacin ne kuma, Deif ya shiga ƙungiyar 'Muslim Brotherhood'.

Deif ya shiga Hamas a lokacin da ta fara a 1987 - bayan boren Falasɗinawa na farko wato intifada.

Hukumomin Isra'ila sun kama shi a 1989, inda ya shafe wata 16 tsare a gidan yari, bisa zargin aiki da sashen soji na ƙungiyar Hamas.

Yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa sashen soji na ƙungiyar Hamas, wato 'al-Qassam'

Haka kuma shi ne ya lura da kafuwar reshen al-Qassam a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

A 2002, Deif ya zama shugaban al-Qassam, bayan kashe shugabanta, Salah Shehadeh a wani hari da Isra'ila ta kai.

A 2015, Amurka ta sanya Deif cikin jerin 'yan ta'addan duniya. Sai kuma ita ma Tarayyar Turai da ta sanya shi cikin jerin 'yan ta'addan a Disamban 2023.

Yunƙurin kashe shi

An zargi Deif ya kitsawa tare da shirya harin bom kan motar bas, wanda ya kashe gomman Isra'ilawa a 1996, tare da hannu a kamawa tare da kisan sojojin Isra'ila uku a tsakiyar shekarun1990.

An kuma yi amanna cewa Deif tare da taimakon Yahya Sinwar - Shugaban Hamas na ke Gaza - suka kitsa harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.

Ana ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen samar wa Hamas makamai: Rokokin Qassam da kuma tonon hanyoyin ƙarƙashin ƙasa a Gaza.

An yi amanna cewa Deif ya shafe mafi yawan lokaci cikin waɗannan hanyoyi na ƙarƙashin ƙasa, don guje wa sojojin Isra'ila tare da shirya hare-haren Hamas.

Wani mutum na daban

A tunnel in Gaza Strip

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi amanna cewa Deif ya shafe mafi yawan lokacinsa cikin hanyoyi na ƙarƙashin ƙasa a Gaza

Ya kasance wani fitaccen mutum, da Falasɗinawa suka sani da mai gwaninta, su kuma Isra'la ke yi masa kallon shu'umin mutum da ke tsallake duk wani tarko da aka sanya masa.

Deif ya tsallake rijiya da baya har sau bakwai tun 2001.

Mafi muni daga cikin yunƙurin kisan da ya tsallake shi ne na 2002, wanda a nan ne ya rasa idonsa ɗaya. Isar'ila dai ta ce ya rasa hannunsa ɗaya da ƙafa, kuma muryarsa ta dishe ta yadda dakyar yake magana.

Deif ya kuma sake tsallake rijiya da baya a wani hari da sojojin Isra'ila suka kai Zirin Gaza a 2014, to amma sun kashe matarsa da 'ya'yansa biyu.

Tun daga lokacin ne kuma aka rage gani ko jin ɗuriyarsa. Hotunansa uku kawai ake da su, ɗayan da na kwnan wata, na biyun kuma ya sanya abin rufe fuska, sai na kuma na ukun wanda shi kuma inuwarsa kawai yake nunawa.