Liverpool ta hada maki uku a kan Bournemouth

An wallafa

An bai wa sabon dan wasan da Liverpool ta dauka a bana daga Brighton, Alexis Mac Allister, jan kati, amma kungiyar Anfield ta ci 3-1 a gasar Premier League ranar Asabar.

Bournemouth wadda ta ci kwallo aka soke sakamakon Jaidon Anthony ya yi satar gida ta fara cin kwallo a minti na uku da fara wasa ta hannun Antoine Semenyo.

Nan da nan kungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama ta kara sa kaimi da ta kai tashi biyu tun kan hutu.

Luis Diaz ne ya fara farke kwallon da aka ci Liverpool, sannan ta kara na biyu ta hannun Mohamed Salah.

Salah ya barar da fenariti, daga nan ne Liverpool ta kara na uku ta hannun Diogo Jota.

Mac Allister, wanda Liverpool ta saya a bana daga Brighton kan fam miliyan 35 ya karbi jan kati kai tsaye, bayan da ya take kafar Ryan Christie.

Da wannan sakamakon Liverpool ta hada maki hudu a wasa biyu, bayan da ta tashi 1-1 da Chelsea, ita kuwa Bournmouuth tana da maki daya a wasa biyu.