Bikin al'ada da hawan dawakai na cikin hotunan Afirka

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya

Mata

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wasu mata kenan tare da 'yan mata bayan da suka sha kwalliya a bikin ranar alu'mmar Amzigh, a Rabat babban birnin ƙasar Morocco ranar Juma'a.
Miji

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mutum kenan ke rera waƙa a lokacin bikin a harabar majalisar dokokin ƙasar, yayin da ƙasar Morocco ke ƙara bai wa al'ummar Amazigh 'yancinsu bayan shekaru masu yawa ana tauye su.
yy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai al'ummar Amazigh masu yawa da ke zaune a ƙasar Algeria, inda wannan matar a ƙauyen Tizi-Ouzou a ƙasar ke murnar zagayowar sabuwar shekarar al'adar ƙabilar da aka fi sani da shekarar "Yennayer".
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Asabar kenan, lokacin da aka yi hawan dawaki a birnin Sokode na ƙasar Togo.
,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yayin da shi kuma wannan matashi ke buga ganga a daɗaɗɗen bikin na al'ada da ake gudanarwa shekara-shekara a Sokode
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A lokacin da ake gudanar da gasar ƙwallon cricket ranar Talata, inda Zurafat Ishimwe wadda ke cikin tawagar ƙasar Rwanda da suka yi nasara kan takwararta ta ƙasar Zimbabwe a gasar ƙwallon cricket ta mata 'yan ƙasa da shekara 19 ta 2023
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Juma'a kuma, wani mai lalular buƙata ta musamman ke tsalle a lokacin atisaye a birnin Alqahira na ƙasar Masar. A kullum ƙungiyarsa na atisaye a ƙoƙarin da take yi na samar da ƙungiyar ƙwallon kafar nakasssu ta kasa a karon farko.
gona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙasar Kenya na amfani da jirage marasa matuƙa wajen yin feshin maganin ƙwari a gona.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Laraba jami'ar jihar Legas a Najeriya ta gudanar da bikin yaye ɗalibai, inda wannan matar ke sanya wa ɗanta hular kammala jami'a a lokacin gudanar da bikin.
ɗalibai

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Inda waɗannan ɗaliban ke duba hotunan da suka ɗauka a bikin.