Liverpool za ta kara da Real da Man City da Chelsea da Arsenal

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Liverpool ta koma ta biyar a teburin Premier League da maki 42, bayan da ta ci Manchester United 7-0 ranar Lahadi a Anfield.

Kungiyar Anfield wadda ta kasa kare kofinta na Carabao da FA Cup a bana, na fatan komawa cikin 'yan hudu farko domin ta buga Champions League a badi.

Sai dai Liverpool tana da wasa masu zafi a gabanta da za ta fafata, domin gani ta yi abin azo a gani a kakar nan.

A bara Liverpool wadda ta yi ta biyu a Premier da kai wa wasan karshe a Champions League ta dauki Carabao da FA Cup.

Liverpool za ta buga wasan Premier League hudu nan gaba masu zafi, bayan da aka dage fafatawarta da Fulham.

Sannan za ta je gidan Real Madrid buga wasa na biyu a Champions League.

Ranar Asabar Liverpool za ta ziyarci Bournemouth a wasan Premier League, kungiyar da Liverpool ta ci 9-0 ranar 27 ga watan Agustan 2022.

Ranar 15 ga watan Maris Liverpool za ta ziyarci Real Madrid a wasa na biyu na zagayen 'yan 16 a Champions League, Real ce ta yi nasara 5-2 a Anfield.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya kamata Liverpool ta buga wasa da Fulham a Anfield a Premier League, amma an dake fafatawar.

Daga nan Liverpool za ta ziyarci Manchester City ranar 1 ga watan Afirilu don buga Premier League, kuma City ce ta biyu a teburi kawo yanzu.

Wasa uku aka kara tsakanin Liverpool da Manchester City:

League Cup Alhamis 22 ga watan Disambar 2022

  • Man City 3 - 2 Liverpool

Premier League Lahadi 16 ga watan Oktoban 2022

  • Liverpool 1 - 0 Man City

Community Shield Asabar 30 ga watan Yulin 2022

  • Liverpool 3 - 1 Man City

Daga nan Liverpool za ta ziyarci Chelsea a wasan Premier, wadanda suka tashi 0-0 ranar 21 ga watan Janairu a Anfield.

Wasa mai zafi da Liverpool za ta kara na gaba shine da Arsenal a Anield ranar 9 ga watan Afirilu, Gunners ce ta yi nasara da ci 3-2 cikin Oktoban 2022.

Jerin wasannin da ke gaban Liverpool yanzu haka:

Premier League Asabar 11 ga watan Maris

  • Bournemouth da Liverpool

Champions League Laraba 15 ga watan Maris

  • Real Madrid da Liverpool

Premier League Asabar 18 ga watan Maris

  • Liverpool da Fulham

Premier League Asabar 01 ga watan Afirilu

  • Man City da Liverpool

Premier League Talata 4 ga watan Afirilu

  • Chelsea da Liverpool

Premier League Lahadi 9 ga watan Afirilu

  • Liverpool da Arsenal