Ƴan Chelsea da za su buga wasannin sada zumunta a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Chelsea ta tsara wasannin sada zumunta a shirin tunkarar kakar 2024/25, domin ta gwada sabbin ƴan ƙwallon da ta ɗauka a bana.
Cikin waɗanda ta ɗauka har da sabon koci, Enzo Maresca da za ta ga kamun ludayinsa da ƴan wasa da suka hada da Tosin Adarabioyo da Kiernan Dewsbury-Hall da Renato Veigaand da kuma Marc Guiu.
Tuni kuma Chelsea ta sanar da ƴan wasa 28 da ta je da su Amurka, domin buga wasannin sada sada zumunta, ciki har da Trevoh Chalobah, mai shekara 25.
Ƴan wasan Chelsea 28 da za su buga mata wasanni a Amurka
Masu tsare raga: Robert Sanchez, Marcus Bettinelli, Eddie Beach, Lucas Bergstrom.
Masu tsare baya: Reece James, Malo Gusto, Josh Acheampong, Wesley Fofana, Axel Disasi, Tosin Adarabioyo, Benoit Badiashile, Levi Colwill, Ben Chilwell, Renato Veiga.
Masu buga tsakiya: Carney Chukwuemeka, Romeo Lavia, Lesley Ugochukwu, Kiernan Dewsbury-Hall, Andrey Santos.
Masu cin ƙwallaye: Nicolas Jackson, Christopher Nkunku, Raheem Sterling, Mykhailo Mudryk, Noni Madueke, Armando Broja, Tyrique George, Marc Guiu, Angelo.
Jadawalin wasannin sada zumunta da suke gaban Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
25 ga watan Yuli : Chelsea da Wrexham a Levi Stadium a Santa Clara
27 ga watan Yuli: Chelsea da Celtic, Notre Dame Stadium a Indiana
1 ga watan Agusta: Chelsea da Club America a Mercedes-Benz Stadium a Atlanta
3 ga watan Agusta: Chelsea da Manchester City a Ohio Stadium a Columbus
7 ga watan Agusta: Chelsea da Real Madrid a Bank of America Stadium a Charlotte
11 ga watan Agusta: Chelsea da Inter Milan a Stamford Bridge
Ƴan wasan da Chelsea ta ɗauka a bana kawo yanzu

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Caleb Wiley - Mai tsaron baya - mai shekara 19, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka shida kan £8.5m daga Atlanta United.
Ɗan wasan tawagar Amurka, za a iya kara masa ƙwantiragin kaka ɗaya.
Tosin Adarabioyo - Mai tsaron baya - mai shekara 26, ya amince da yarjejeniyar kaka huɗu daga Fulham, wanda ya fara daga makarantar koyon tamaula ta Manchester City.
Omari Kellyman - Mai buga tsakiya - mai shekara 18, ya koma Stamford Bridge daga Aston Villa £19m. Ya buga wa Ingila tamaula ta ƴan kasa da shekara 20.
Marc Guiu - Mai cin ƙwallaye - mai shekara 18, mai ƙunshin yarjejeniyar Yuro miliyan shida, inda Barcelona ta so kara tsawaita zamansa, amma ya zabi komawa Chelsea kan yarjejeniyar kaka biyar.
Ya ci wa Barcelona ƙwallo uku a wasa biyar da ya buga wa babbar ƙungiyar tamaula.
Kiernan Dewsbury-Hall - Mai buga tsakiya - mai shekara 25, ya koma Chelsea daga Leicester City, inda sabon koci, Enzo Marresca ya sa aka sayo shi kan £30m kan yarjejeniyar kaka shida.
Renato Veiga - Mai tsaron baya/Mai buga tsakiya - mai shekara 20, ya koma Chelsea daga Baselkan kan yarjejeniyar kaka bakwai kan £12m, wanda zai iya taka leda a matakin mai tsaron baya ko mai buga tsakiya.
Estevao Willian (Sai kakar badi zai koma Stamford Bridge) - Mai buga gefe - mai shekara 17, wanda ta ɗauka daga Palmeiras kan £29m.











