Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Karota na neman ɗan a-daidaita-sahun da ya ɗauko kurar da ta kubuce a Kano
Hukumar kula da sufurin mota a jihar Kano (KAROTA) ta ce tana ci gaba da neman wani mai baburin a-daidaita-sahu ruwa a jallo bayan ya ɗauko wata kura da ta yi ƙoƙarin tserewa a tsakiyar kasuwa.
Hukumar ta ce jami'anta suna neman mai a-daidaita-sahun saboda abin da ya yi ya saɓa wa doka, don kuwa bai kamata ya ɗauko dabbar daji a cikin babur ba.
Mai magana da yawun hukumar, Nabulisi Abubakar ya shaida wa BBC cewa kura ba tunkiya ko akuya ba ce, dabba ce mai hatsari da bai kamata a bar ta tana gararamba a cikin mutane ba.
“Muna ci gaba da neman ɗan a-daidaita-sahun a yanzu haka, kuma muna da lambobin babura guda biyu da muke zargi, matuƙar kuma muka kama direban, to kotu za mu kai shi kai tsaye.
Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a kasuwar 'yan canji ta Wapa da ke tsakiyar birnin Kano, daidai lokacin da mutane ke gudanar da harkokin rayuwa da suka saba.
Kurar dai wadda aka ɗauko a cikin a-daidaita-sahu ta yi yunƙurin ƙwacewa ne lokacin da ta kufce daga hannun mai ita wanda fasinja ne a tsakiyar kasuwar.
Hakan dai ya yi matuƙar ta da hankulan mutanen da suka fara gudu a tsakiyar kasuwa a daidai lokacin kurar ta fara watayawar samun 'yanci.
Shugaban kasuwar 'yan canji, Hussaini Abdullahi ya ce kurar ta ƙwace ne jim kaɗan bayan sun gama sallar la'asar, lokacin da baburin a-daidaita-sahun da ya ɗauko kurar yaker wucewa.
A cewarsa, takunkumin da aka sanya wa kurar ya cire abin da ya sa mutane suka ƙara tsurewa ke nan.
“Duk da haka wasu masu taurin kai sun tsaya suna kallon abin da ke faruwa, yayin da wasu suka sheƙa da gudu. Allah dai ya kiyaye kurar ba ta fara bin mutane da gudu ba".
Ya ce daga bisani ne mai kurar ya yi nasarar sake kama ta har ma ya mayar da takunkumin bakinta, kafin ya ɗauke ta su ci gaba da tafiya.
Hussaini Abdullahi ya ce: "a lokacin ba su san hukuma na neman mai a-daidaita-sahun ba, don kuwa ya zo ne kawai ya wuce ta WAPA.
Manajan gidan ajiye namun daji na jihar Kano, Nura Lawal ya ce masu fataucin namun daji ya kamata a fi mayar da hankali wajen hukuntawa saboda abin da suke yi tozarta dabbobin daji ne. A cewarsa, jami'ansa sun yi ƙoƙarin kama kurar da mai ita bayan sun ji labarin abin da ya faru, amma kafin su je WAPA, sun gudu.
“Muna jin labarin cewa kura ta ƙwace, sai muka tashi jami'anmu waɗanda ƙwararru ne wajen tu'ammali da namun daji su je su kamo ta, amma suka yi rashin sa'a.”
Ya ce abin da irin waɗannan mutane masu yawo da namun daji ke yi, ya saɓa wa doka saboda yin hakan fataucin dabbobin daji kuma doka ta tanadi hukunci kan masu aikata irin wannan laifi.
Da mun gan shi, in ji Nura Lawal kama shi za mu yi mu gurfanar da shi a gaban kotu saboda abin da ya aikata.
Manajan ya ƙara da cewa ”Ganin sun ɗauko kura a cikin baburin a-daidaita-sahu maimakon abin hawa na musamman da ake amfani da shi wajen sufurin irin waɗannan namun daji, ya nuna cewa mutanen ba su san yadda ake tarairayar irin waɗannan dabbobi ba".
Wasa da kura daɗaɗɗiyar al'ada ce a ƙasar Hausa
Sana'ar gardi mai wasa da kura, daɗaɗɗiyar al'ada ce a tarihin ƙasar Hausa. Masu wannan sana'a suna kamo kura ne su ɗaure ta da igiya sanye da takunkumi suna yawo a cikin gari ko kasuwanni suna wasa da ita, ana ba su kuɗi.
Haka kuma tsawon shekaru, masu irin wannan sana'a suna ba da magungunan gargajiya kamar maganin fitsarin kwance ga ƙananan yara da maganin farin jinin 'yan mata da sauransu.
Wani mai sharhi kan rayuwar al'umma a Kano, Shuaibu Sani ya ce sana'ar wata tsohuwar al'ada ce da ya kamata a ce an kawo ƙarshen ta saboda hatsarin da take tattare da shi.
“Kamata ya yi ma gwamnati ta hana wasa da kura kuma ta haramta wa masu tallar magungunan gargajiya amfani da namun daji don tallata hajarsu,” in ji Mallam Shu'aibu.