Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda muggan namun daji ke tare manyan hanyoyin Najeriya
Namun daji kamar yadda masana suka bayyana kan yi ƙaura ko kuma yin tafiya mai nisan zango daga daji zuwa daji domin biyan bukatunsu na rayuwa.
Sai dai a yayin da suke kokarin yin hakan ne sukan shiga hurumin bil'adama, inda sukan mamaye hanyoyi da burtalin dabbobin gida da gonaki a wasu lokutan ma da kauyukan jama'a.
Akan samu irin wannnan a kasashe da dama musamman wadanda ke da gandun dazuka da kuma namun daji da yawa.
Haka kuma, akwai kasashen da za ka ga suna da budaddun kan iyakoki da ke saukaka wa muggan namun dajin yin dogon zango da kuma shiga wasu kasashen su kuma fita a duk lokacin da suka ga dama.
Najeriya na daga cikin kasashen da Allah ya azurta da gandun dazuka a yankuna daban-daban, kuma a shekarun baya an yi ta samun bullar manyan namun daji a wasu manyan titina, da kauyuka da wasu gonaki.
Sai dai sannu a hankali yawan haduwar da mutane ke yi da su musamman mafarauta da direbobi ya ragu.
Hakan dai ba ya rasa nasaba da irin yadda masana ke cewa yawansu na kara raguwa a gandun dazukan saboda dalilai da dama.
A nau'ukan dabbbobin dajin da suka fi kaura da kuma tafiya mai nisan zango akai-akai su ne giwaye, wadanda kan fita a garke-garke, amma a wasu lokutan an bayyana cewa zakuna kan yi irin wannan fita sai dai ba kamar giwayen ba.
Giwayen dai su ne suka fi yawan fitowa kan manyan titknan arewacin Najeriyar yayin da suke kan hanyar su ta bulaguro.
A makonnin baya ma an samu bullar garken giwayen a garin Rann da ke yankin karamar hukumar Kala Balge arewacin jihar Borno, inda suka firgita mazauna garin tare da lalata musu amfanin gona.
Mahukuntan jihar sun ce giwajen sun fito ne daga gandun dajin kasar Kamaru, kuma suna yawan shigowa daga can, musamman ma da yake kan iyakokin a bude suke.
Baya ga garin na Rann, akwai kauyen Izge da ke karamar hukumar Gwoza a kudancin jihar Borno wanda shi ma ya yi kaurin suna wajen yawan kai farmakin giwayen da kan tattake amfanin gona da ma wasu bukkokin mutane.
A jihar Yobe ma mai makwabtaka da jihar Borno akan samu bullar namun dajin, amma kuma na giwayen a nan ma ya fi yawa, inda ko a shekarun baya sun taba ratsowa ta kan babbar hanyar Damaturu zuwa Potiskum a jihar, inda suka tayar da hankulan masu ababen hawa da kuma masu gidaje da gonaki a kusa da hanyar.
Malam Abba Musa da aka fi sani da Abba Lion, wani marubuci ne kuma mai harkar sufuri da ke garin Nguru na jihar Yobe, kuma yana daya daga cikin wadanda suka taba gane wa idanunsu yadda ayarin giwayen suka bulla a yankin nasu a shekarun baya.
Ya shaida wa BBC cewa ya ga abin mamaki da bai taba gani ba game da giwaye, a lokacin da suka hau kan kwalta da niyyar ketarawa.
''Garken giwaye ya biyo ta tsakanin babbar hanyar Damaturu zuwa Potiskum suka ketaro ta kan kwalta a kan hanyarsu ta daga wuri mai nisa a kan hanyarsu ta komawa kasar Kamaru, sun ci karo da wata babbar mota da ta yi lodin kanwa daga garin Gashua ta lalace, sai babban toron giwar ya zo cikin motar ya sansana buhunan kanwar da hancinsa ya dauko buhun kanwar ya doka shi da kasa buhun ya fashe suka zo suka rika lasar kanwar."
Daga bisani ne in ji Abba giwayen suka tsallaka hanya daga arewa zuwa kudu, a lokacin ne jama'a da dama har da jami'an tsaro, da jami'an gwamnatin jihar suka yi tururuwa zuwa wurin don gane wa idanunsu.
''Ni ma da kai na na debi mutane a motata, muka dunguma, a nan ne na ga wani dan jarida dauke da wata doguwar na'urar daukar hoto, ya tsuguna zai dauki hoton giwayen kenan sai toron giwar ya yi wani kara mai karfin gaske, ya nufi mai daukar hoton, a nan ne mutane kowa ya ruga da gudu.
Wani abin mamaki sai giwayen suka rabu gida hudu wasu na kallon gabas, wasu yamma, wasu kudu, wasu kuma arewa, wanda da alamu suna kare kan su ne.
''Tun da nake ban taba ganin giwaye masu girma irin wadannan ba,'' in ji shi
Ya ƙara da cewa giwayen sun dau hanya suka yi kudu..suka kara gaba daga nan sai jama'a suka dawo.
Wadannan yankuna suke yi da kasar ta Kamaru inda aka bayyana ta nan ne giwayen kan taso har su dangana ta cikin dazuwa su bullar har zuwa jihar Yobe mai makwabtaka da jihar Borno.
A watan Agustan shekara ta 2018 ma an bayar da labarin yadda wasu giwaye uku da aka bayyana sun kubuto daga wani gandun daji a jamhuriyar Nijar suka ka kai farmaki a karamar hukumar Koko Besse a jihar Kebbi. Mazauna yankin suka ce akwai yiwuwar sun kai farmaki kauyen ne bayan bacewar da ragowar 'yan uwansu da suka taho tare suka yi musu, inda har sai da jami'an tsaro suka kai musu dauki.
Gandun dazuka a arewacin Najeriya
Akwai gandun dazuka da dama a Najeriya, inda a yankin arewacin kasar akwai gandun dajin Yankari a jihar Bauchi, Gashaka Gumti a jihohin Taraba da Adamawa, da na Kamuku a yankin Birnin Gwari jihar Kaduna, da Cingurmi Duguma da Dagona a jihar Yobe wadanda su ne tsayayyun gandun dazukan da gwamnati ke kulawa da su, da kuma namun daji da ake kiwon su.
Wadanda suka fi shahara su ne Gashaka Gumti da kuma Yankari
Shin me yake saka namu daji shigowa cikin jama'a?
Mutane da dama na ganin cewa namun daji suna yin abu da ka ne, amma kuma in ji masana halayyar dabbobin daji batun ba haka yake ba, suna amfani da kwakwalwarsu fiye da yadda dan adam ke tunani.
Mr Stephen Zailani Haruna masani ne kan harkokin raya gandun dadi a Najeriya, ya kuma shaida wa BBC cewa duk wata dabbar daji bukatunta ba su wuce uku ba, abinci, ruwan sha, da wurin fakewa kamar idan ya ji motsin da bai yarda da shi ba, ko kuma inda zai kwanta ya huta.
Abubuwa guda ukun nan su yake nema, Don haka ya kan yi tattaki domin ya samu irin abinda take so. Ya ce don hake ne su kan yi kaura, har su yi tafiya mai nisa don biyan wadannan bukatu.''
''Abin da ke faruwa shine, yawanci inda dabbobin dajei suke a da sukan zagaya su uje wuri da nisa su yi cirani har su yi tafiya mai dogon zango su je wuri da nisa su yi shekara daya zuwa biyu sannna su dawo, lokacin akwai dazuka ko ta ina, komai suke nema za su same shi, daga wannan gandun daji zuwa wancan. Su ba su san iyaka ba, duk daji daji ne a wurinsu, mu ne biladama muke iyakancewa.'' In ji Stephen.
Mr Stepen ya kuma bayyana cewa a duk gandun dajin da dabobin suka yada zango, sauran dabobobn su kan yi marhaba da su musamman ma idan jinsi daya ne.
Wadannne suka fi yin tafiya mai dogon zango?
Masanin ya kuma kara sahida wa BBC cewa a cikin namun daji, giwaye su ne suka fi yawan yin tafiya mai dogon zango, saboda ita giwa na bukatar abinci sosai a ko wane yin.
''Saboda tana da girma da karfin da za ta iya taka wa har na tsawon kilomita fiye da hamsin a yini guda tana yawon neman abinci, kuma galibi giwaye su kan tafi ne cikin garke kamar ko wace zuriyar dabbob'', mazan idan suka kasaita su kan fice daga cikin garke su je su kafa nasu garken.''
Kamar yadda wasu ke cewa giwaye na kai musu farmaki kuwa, Mr Stephen cewa ya yi mutane ne ba su fahimci halayyar ta ba, domin ita giwa tana iya tuna abu sosai, don haka muddin aka wuce da ita ta wuri tun tana karama, to ko zai mkai shekaru 50 ba za ta manta ba.
Shi yasa a yayin da mutane ke ganin giwaye na yi musu kutse, su kuma suna ganin mutane ne ke mamaye musu hanyoyin da suke bi idan bukatar hakan ta taso.
''Giwaye na rayuwa su kai shekara 75 zuwa 80 ko ma fin haka, kamar dai dan adam, a duk inda aka taba bi da su tun suna kanana ba za su manta da wurin ba,ko da kuwa sun shekara 20 ne ba su bi ba.
Amma saboda gonaki sun karu, gine-gine sun karu, an kafa sabbin kauyuka a hanyoyin da suka saba bi, idan bukatar su ta zo za su sake biyowa su bi ta kai, wanna shi ne ke kawo rashin jituwa tsakanisu da mutane.''
Wasu manoma sun ce giwaye ba sa son su ji ihu ko hayaniy shi yasa suke fitowa suna ta ihu don su kori giwajen daga shigowa gonakinsu...
Ai ya zama kamar ana razana su ne, idan suka fahimci haka sai su juya, idan aka dauki bindigar toka, ko ana buga garwa, ko ihu dole su juya. Dole ya daga musu hankali.
Masanin dai ya ce galibi idan irin wadannan namun dajin na wucewar da suke yi ba su cika damuwa da mutane ba, idan dai ba matsarsu aka yi ba.''
''A yan shekarun baya akan samu giwaye da kan taso daga dajin yankari su yi arewa su dangana da hanyarda ta taso daga Bauchi zuwa Gombe, har akan samu haduran motoci a kan hanya da dare, akan samu wannan amma jifa jifa,'' sun fi fita da dare saboda ba bu mai damunsu sosai, amma inda ba su da matsala da rana ma su kan yi yawon su.'' ya ce.
Zakuna
An samu haka ya dade da faruwa a lokacin da zakoki suka fito suka mamaye kan titina wasu biranen dakew kusa da gandun dajin a arewacin Najeriya, yanzu ba sosai ba saboda yawansu ya ragu matuka in ji masanin, amma kuma kamar a baya ba.
Zakuna kuwa in ji masanin duk da cewa a shekarun baya ana samun labarin bullarsu kan titinan wasu biranen dakew kusa da gandun dajin a arewacin Najeriya, yanzu ba sosai ba saboda yawansu ya ragu matuka.
'' Duk dabba da kika sani mutum ya fi karfinsa, ko da zai iya kashe mutum, yana tsoron dan adam,sai dai in ya zamar musu dole su tunkari dan adam don su kare kan su,'' Kamar irin su zakuma sauran dabbobi sune abincin su, sai ya zama dole ne suke far wa mutane.''
Wata kididdiga ta nuna cewa ainihin zakunan dawa ba a samunsu sosai a Najeria sai kamar a dazukan Yankari da kumana Kainji Lake a Najeriya. Amma kuma bayanai sun nuna cewa galibi saboda masu farautarsu ba bisa ka'ida ba, da kuma halayyara wasu makiyaya da kan saka musu guda don kada su rika kashe musu dabbobi ya haifar da karancinsu.
''Da yake ba su da yawa yanzu yana da wahala su fita manyan titina, ''. sai dai titinan da ke iya cikin gandun dajin Yankari da na Kainji Lake di.'' Stephen ya ce.
Kuraye
Kuraye na daga cikin namun dajin da a shekarun baya suka fi shiga cikin mutane, inda sukan fito daga dazuka neman abinci. Su kan shiga gonaki da kuma kauyukan dake kusa da gandun daji.
Mr Stephen Zailani ya yiwa BBC karin bayani cewa ana samunsu a wurare da dama baya da dazukan Yankari da sauran gandun dazuka, kuma su kan yi farauta amma ba kamar sauran namun daji ba.
'' Da yake su ba su cika kashe dabba ba, su kan jira sai an kashe sannnan su samu su ci, amma kuma a wasu lokutan sukan kashe, kuma galibi sun fi fita da dare.''
Me ya kamata mutane su yi game da namun dajin?
Duk da cewa namnun daji yawansu ya ragu ta yadda ba kasafai su kan fito cikin jama'a ba, amma kuma mutane kan yi gonaki a kusa da gandun da zauka, kamar yadda masanain ya shaida wa BBC.
Ya ce a kan yiwa mutane gargadi da suka rika nesa da gandun daji, kuma su rika sanar da hukuma idan suna fuskantar barazana ko barna daga namun daji, kada su ce za su kashe su.
'' Mutane kan matsi namun dajin, wanda hakan ya sa ake ganin suna shiga hurumin jama'a, ''wasu gonakin sun zo har kan iyakar gandun dazuka."