Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta kammala sayen Cucurella daga Brighton
Chelsea ta kammala daukar dan kwallon Sifaniya mai tsaron baya Marc Cucurella daga Brighton kan fam miliyan 50.
Tun farko an dauka dan wasan mai shekara 24, zai koma taka leda a Manchester City, wadda taki taya dan kwallon da tsoka.
Cucurella ya yi kaka daya a Brighton da buga mata wasa 35 da cin kwallo daya, bayan da ya koma Ingila da buga tamaula daga Getafe.
Ya zama na uku da Chelsea ta dauka a bana, bayan Raheem Sterling da mai tsaron baya, Kalidou Koulibaly.
Haka kuma kungiyar Stamford Bridge ta amince da farashin fam miliyan 20 da Aston Villa ta gindayawa matashin dan kwallon Ingila, Carney Chukwuemeka.
A makon jiya Brighton taki sallama tayin fam miliyan 30 da Manchester City ta yi wa Cucurella.
Tun farko Brighton ta yi wa dan kwallon nata farashin fam miliyan 50, kamar yadda ta sayar da Ben White a bara ga Arsenal.
Shi ne na biyu da ya bar Brighton a kakar nan, bayan Yves Bissouma da Tottenham ta dauka kan fam miliyan 25.
Wanda ya fara kwallo daga makarantar koyon tamaula ta Barcelona ya yi wa babbar tawagar Sifaniya wasa daya, ya buga wa matasan kasar 'yan shekara 23 wasanni a Tokyo Olympic Games da Sifaniya ta yi ta biyu.