Liverpool ta fara da rashin nasara a hannun Forest a bana

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

A karon farko Liverpool ta yi rashin nasara a Premier League ta bana, inda Nottingham Forest ta ci 1-0 a Anfield ranar Asabar.

Callum Hudson-Odoi ne ya ci ƙwallon da ya bai wa Forest maki ukun da take bukata a wasan mako na huɗu a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Shi ne wasan farko da ƙungiyar Anfield ta yi rashin nasara a kakar nan, bayan da ta fara doke Ipwich da Brentford da kuma Manchester United da haɗa maki tara.

Wannan shi ne wasan farko da Forest ta yi nasara a Anfield tun bayan 1969 a dukkan gasa.

Rashin nasara ta farko a Anfield tun bayan 14 ga watan Afirilun 2024 da Crystal Palace ta je ta ci 1-0, tun kan nan Atalanta ta doke Liverpool 3-0 a gida a Europa League ranar 11 ga watan Afirilun 2024.

Da wannan sakamakon Forest ta koma ta huɗun teburi, bayan cin wasa biyu da canjaras biyu, Liverpool kuwa mai maki tara tana matakinta na biyu.

Ranara Talata 17 ga watan Satumba, Liverpool za ta je Milan, domin buga wasan farko a rukuni a Champions League.

Daga nan Liverpool za ta buga wasan mako na biyar a Premier League a Anfield, inda za ta karɓi bakuncin Bournemouth.

Ita kuwa Forest za ta je gidan Brighton, domin karawa a mako na biyar a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar 22 ga watan Satumba.