Brighton ba ta da niyyar sayar da Caicedo a wannan bazarar

Asalin hoton, Getty Images
Brighton na sa ran cewa Moises Caicedo zai ci gaba da kasancewa a kungiyar idan aka rufe kasuwar cinikin 'yan wasa a ranar 1 ga Satumba.
Dan wasan dai ya kasance kan gaba cikin 'yan wasan da suka yi zawarci a bazarar nan bayan Arsenal ta nuna sha'awarta a watan Janairu.
Babu kungiyar da ta taya dan wasan kan farashin da Brighton ta kayyade kawo yanzu.
Brighton ta dage kan cewa ba sa son sayar da dan wasan na kasar Ecuador mai shekara 21, kuma ba su da bukatan yin hakan bayan ficewar Alexis Mac Allister zuwa Liverpool.
An sanar da Caicedo game da wannan matsayin kuma Brighton ba ta yi tunanin haka zai zama matsala ba.
Dan wasan ya nemi barin kungiyar a watan Janairu sakamakon zawarcin Arsenal.
Brighton ta ki amincewa da haka, sai Caicedo ya sanya hannu kan sabuwar kwangila a cikin watan Maris wanda zai gudana zuwa 2027.
A wannan bazarar, Brighton ta yi watsi da tayin Chelsea guda biyu na Fam miliyan 70 da 80.
Brighton ta samu gurbin shiga gasar cin kofin Europa League bayan da ta kare a mataki na shida a gasar Firimiya a bara.











