Chelsea ta kai zagayen kwata fainal a Champions League

Raheem Sterling

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Chelsea ta doke Borussia Dortmund da ci 2-0 a wasa na biyu zagayen 'yan 16 a Champions League da suka fafafata a Stamford Bridge.

Daf da za a je hutu Chelsea ta ci kwallo ta hannun Raheem Sterling, daga nan ta kara na biyu a bugun fenariti ta hannun Kai Havertz a minti na takwas da komawa zagaye na biyu.

Kenan Steerling yana da hannu a cin kwallo 44 a Champions League ya ci 27 ya bayar da 17 aka zura a raga, tun bayan da ya fara buga gasar a Satumbar 2014.

Wayne Rooney tsohon dan wasan Manchester United, shine a Ingila mai kwallo 30 a raga a gasar ta zakarun Turai.

Ranar 15 ga watan Janairu, Dortmund ta ci Chelsea 1-0 a wasan farko a gasar ta zakarun Turai da suka yi a Jamus.

Chelsea ta kai wasan daf da na kusa da na karshe da cin kwallo 2-1 gida da waje kenan.

Kungiyar Stamford Bridge, wadda take ta 10 a teburin Premier League na fuskantar koma baya a kakar nan.

An fitar da ita a FA Cup na kakar nan, ba ta kai bante ba a Carabao Cup, wanda Manchester United ta lashe.

Tun bayan kammala gasar kofin duniya, Chelsea ta kasa cin wasa da yawa, wadda ta doke Bournemouth da Crystal Palace da kuma Leeds United.

Ranar Asabar 11 ga watan Maris Chelsea za ta ziyarci Leicester City domin buga Premier League a King Power.