Man United ta kusan kammala ɗaukar Yoro daga Lille

Leny Yoro

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta kusan kammala ɗaukar mai tsaron bayan Lille, Leny Yoro.

Wata majiya ta ce United ta amince za ta biya £52.06m kuɗin Yoro, wanda ke shirin zuwa Manchester ranar Laraba, domin auna koshin lafiyarsa.

Mai shekara 18 yana cikin matasa masu tsare baya da manyan ƙungiyoyin Turai suka nuna sha'awar sayen shi, ciki har da Real Madrid.

Yoro, wanda ya fara buga wa Lille tamaula yana da shekara 16, yana cikin waɗanda Thierry Henry ya sanar na ƙwarya-ƙwarya, domin yi wa Faransa tamaula a Olympic.

Daga baya aka fitar da shi daga tawagar, bayan da Lille za ta buga wasannin neman gurbin shiga gasar Champions League ta bana.

Zuwansa Ingila zai kara sabbin jini a gurbin masu tsare baya a Manchester United.

Everton ta ƙi sallama tayi biyu da United ta yi wa Jarrad Branthwaite, bayan da ƙungiyar Goodison Park ta ce ƙudin ɗan wasan ya kai £75m.

Haka kuma United na tattaunawa da Bayern Munich kan ɗaukar ɗan wasan Netherlands, Matthijs de Ligt.

Wata majiya ta ce bayan da United ke batun ɗaukar Branthwaite da De Ligt, ba za ta sayi ƴan wasan biyu ba a tare sai dai ɗaya, sannan kafin ta sake ɗaukar ɗan ƙwallo ya hada da ƙudin da take da shi a kasa.

Raphael Varane ya bar United a karshen kakar da ta wuce, sannan ana tantama kan makomar ɗan wasan tawagar Sweden, Victor Lindelof, wanda yarjejeniyarsa zai kare a karshen kakar da za a fara.

Ƙungiyoyn Premier League da yawa sun yi kokarin ɗaukar Harry Maguire a bara, amma ya ƙi amincewa ya bar United, wanda ya buga wasa 22 a kakar da ta wuce.

Joshua Zirkzee, mai shekara 23, shi ne na farko da United ta ɗauka a bana a makon jiya, kan £36.5m daga ƙungiyar Bologna ta Italiya.

Haka kuma United ta amince za ta karɓi £27m daga Marseille ta bayar da Mason Greenwood, yayin da mai tsaron baya, Willy Kambwala ya bar Old Trafford zuwa Villarreal kan ƙudin da ya kai £9m.