Man City ta hau teburin Premier bayan casa Southampton

An wallafa

Manchester City ta dare mataki na daya a kan teburin Premier League, bayan da ta doke Southampton 4-0 ranar Asabar a Eihad.

City ta ci kwallo a minti na 20 da fara wasa ta hannun Joao Cancelo, minti 12 tsakani Phil Foden ya ci na biyu na biyar da ya zura a raga a kakar nan.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne City ta ci gaba da cin kwallo ta hannun Riyad Mahrez, sannan Erling Haaland ya kara na hudu na 15 da ya ci a bana.

Da wannan sakamakon City ta koma ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 23, bayan buga wasa tara.

Arsenal za ta iya karbar gurbinta, wadda za ta karbi bakuncin Liverpool a Emirates a karawar maki na tara mai maki 21.

Liverpool wadda ta yi wasa bakwai tana ta 10 da maki 10, kafin tashi wasan Brighton da Tottenham da ake yi ranar Lahadi da yammaci.