Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
World Cup 2022: An kira Ronaldo a tawagar Portugal da za ta Qatar
Cristiano Ronaldo da ke neman hannu a Manchester United a wannan kakar ya samu shiga cikin 'yan wasa 26 da Portugal ta kira za su buga mata gasar duniya a Qatar.
Dan wasan mai shekara 37 ya yi wasa 16 a wannan kakar, an fara 10 da shi sannan ya ci kwallo uku kacal.
"Duka 'yan wasan da aka kira suna da yunwar samun nasara tare da mayar da Portugal gwarzuwar duniya, kuma Ronaldo yana cikinsu," in ji kocin Portugal Fernando Santos.
Akwai yan wasan 10 cikin tawagar da dukakkansu suka fito daga gasar Premier.
Abokan taka ledar Ronaldo a Manchester Bruno Fernandes da Diogo Dalot sai 'yan wasan City da suka hada da Joao Cancelo da Ruben Diaz da kuma Bernardo Silva.
An zabi dan wasan Fulham Joao Palhinha da 'yan wasa uku daga Wolves da suka hada da Jose Sa da Ruben Neves sai kuma Matheus Nunes.
Sai dai a wanna karon ba a kira tsohon dan wasan tsakiya na kasar ba Joao Moutinho da ke taka leda a Wolves da abokin kwallonsa Goncalo Guedes.
An bar dan wasan Paris St-Germain Renato Sanches a baya ba a tafi da shi ba.
Portugal za ta je gasar babu dan wasan gaba na Liverpool da ke fama da rauni Diogo Jota amma an kira Pepe daga Porto da ke da shekara 39.
Portugal da ke rukunin H za ta fara wasanta na farko da Ghana a ranar 24 ga watan Nuwamba.
Tawagar Portugal
Masu tsaron raga: Diogo Costa (Porto), Rui Patricio (AS Roma), Jose Sa (Wolverhampton Wanderers)
'Yan wasan baya : Joao Cancelo (Manchester City), Diogo Dalot (Manchester United), Ruben Dias (Manchester City), Raphael Guerreiro (Borussia Dortmund), Nuno Mendes (Paris St-Germain), Pepe (Porto), Danilo Pereira (Paris St-Germain), Antonio Silva (Benfica)
'Yan wasan tsakiya : William Carvalho (Real Betis), Bruno Fernandes (Manchester United), Joao Mario (Benfica), Ruben Neves (Wolverhampton Wanderers), Matheus Nunes (Wolverhampton Wanderers), Otavio (Porto), Joao Palhinha (Fulham), Bernardo Silva (Manchester City), Vitinha (Paris St-Germain)
'Yan gaba: Joao Felix (Atletico Madrid), Ricardo Horta (SC Braga), Rafael Leao (AC Milan), Goncalo Ramos (Benfica), Cristiano Ronaldo (Manchester United), Andre Silva (RB Leipzig)