Shin ƙarya, yaudara da cin amana ne manyan shika-shikan siyasa?

...

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa

Siyasa na ci gaba da samun ma'anoni da fassara iri-iri daga bakunan 'yan Najeriya.

Watakila wannan ba ya rasa nasaba da yadda ake ganin wasu na nuna wasu dabi’u na assha ko dai kafin zabe ko kuma bayansa.

Ita dai siyasa na nufin hanyoyin da za a bi a samar da shugabanci, a kuma gudanar da shuganbanci na gari, kamar yadda dakta Sa'idu Ahmad Dukawa na Jami'ar Bayero da ke Kano ya bayyana.

Haka kuma siyasa na nufin hanyoyin da za a bi a samar da shugabanci, a kuma gudanar da shuganbanci na gari.

To sai dai al'ummar Najeriya na kallon siyasa a matsayin wadda ke kunshe da munanan siffofi, da suka hada da karya da cin amana da yaudara da munafurci da sauransu.

Daga cikin masu irin wannan ra'ayi har da malaman addini, waɗanda a lokuta da dama ke alaƙanta siyasa da wadannan munanan siffofi.

Har ma a wasu lokuta wasu ke sukar malaman addinan idan suma tsunduma cikin siyasa.

Wanne ne ma ya sa mafi yawan malaman addini ke kokarin kaurace wa siyasar, saboda mummunan fahimta da ake ci gaba da yi mata.

Me ya sa 'yan Najeriya ke alakanta siyasa da munanan dabi'u?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To ko mene ne masana harkokin siyasa ke cewa game da wannan ikirari?

Farfesa Abubakar Kari, malami a jami'ar Abuja ya ce al'amura ne suka lalace shi ya sa mutane suka fara yi wa siyasa mummnar fahimta, musamman a Najeriya.

Amma ya ce siyasa ta fara gurɓacewa ne a baya-bayan nan a Najeriya, domin kuwa a baya ba haka abin yake ba, musamman lokacin siyasar neman 'yancin kai da ma jamhuriya ta farko da ta biyu.

''Abin da ya sa kuma shi ne su waɗancan 'yan siyasar na farko sun gina siyasar tasu ne kan aƙida da ci gaban ƙasa, sannan kuma ba a amfani da abubuwa da dama da a yanzu ake amfani da su , shi yasa al'ummar wancan lokaci suka yi amanna da siyasa'', in ji malamin jami'ar.

Ya ce amma sannu a hankali al'amura suka riƙa lalacewa, har sai da ya kasance jam'iyyu da 'yan siyasa ba su da wata cikakkaciyar aƙida a ƙasar.

Dakta Sa'idu Ahmad Dukawa ya ce abin da ya janyo mutane ke bai wa siyasa wannan fassara shi ne yadda 'yan siyasar ke bayar da hoton kansu ta hanyar halayyarsu, inda ma a wasu lokuta suke ambata da bakunansu.

''A wasu lokutan 'yan siyasar da kansu ke cewa ai siyasa ba ta rabo da ƙarya da cin amana da yarfe da zamba da maguɗi da munafurci da makamantansu'', in ji shi.

Masanin ya ƙara da cewa a wasu lokuta su 'yan siyasar da kansu ke cewa, ''idan mutum yana so a tono asirin iyaye da kakanninsa to ya shiga siyasa''.

Dakta Dukawa ya kuma ce mafi yawan ayyukan 'yan siyasar na nuni da ire-iren waɗannan ɗabi'u da halaye.

''Ba sa jin komai su yi alƙawari su saɓa, ba sa jin komai su yi rantsuwa a kan ƙarya, ba sa jin komai a ba su amana su ci'', in ji Malamin jami'ar Bayeron.

b

Yadda ƙasashen duniya ke kallon siyasa

Dakta Dukawa ya ce a ƙasashen duniya da dama ma ana yi wa siyasa makamancin wannan kallo.

Ko ina akan yi bi-ta-da ƙullin siyasa da zarge-zargen laifukan da suka shafi rashawa daga ɓangaren 'yan siyasa, sai dai kawai bambancin hukunci tsakanin ƙasashe.

''A wasu ƙasashen in an kama ɗan siyasa da laifi da wuri ake ɗaukar matakai a kansu, sabanin wasu ƙasashen da sai a daɗe ba a hukunta mutanen da aka kama da laifukan cin hanci ba'', in ji Dakta Dukawa.

Shi ma Farfesa Kari ya ce siyasa ta fara fita daga zukatan mutane a ko ina cikin faɗin duniya sakamakon wasu munanan halaye da 'yan siyasa ke aikatawa.

''Ko a Amurka idan ka lura za ka ga cewa idan aka yi zaɓe mutanen da ke fitowa domin kaɗa ƙuri'unsu ba su kai rabin al'ummar ƙasar ba, wannan kuma ba ya rasa nasaba da irin dawo daga rakiyar 'yan siyasa da al'umma ke ci gaba da yi'', in ji shi.

Mece ce alaƙar siyasa da addini?

A ilimance siyasa ita ce ƙololuwar daraja da ya kamata mutum ya yi ta fuskar mulki ko wakilci, kamar yadda Dakta Dukawa ya bayyana.

Ya ce a musulunce da Allah ya aiko annabi Adamu A.S ya kira shi da 'Khalifa' wato wanda zai wakilce shi a doron ƙasa, wajen kula da halittun Allah S.W.T

''To wanda ke kula da duka halittun Allah kuwa ai shi ake kira da siyasa.''

Ya kuma ce Annabi Muhammad ya ce su Yahudawa annabawansu su ne 'yan siyasarsu wato shugabanninsu ''to ka ga tunda aka alaƙanta siyasa da annabta to ka ga ƙololuwar daraja ke nan da ɗan'adam zai samu''.

''Abin da addini ke ƙoƙarin yi na kare haƙƙoƙin mutane da sauran halittu, shi ne ya kamata siyasa ta yi don kare wa mutane haƙoƙinsu'', in ji Dakta Dukawa.

Mene ne siffofin siyasa a ilimance?

A bisa tsarin kimiyyar siyasa, siyasa na nufin mutane su haɗu domin samar da shugabanci da zai yi jagoranci domin kare musu muradunsu. Don haka Dakta Sa'idu Ahmad Dukawa ya ce akwai siffofin siyasa da suka haɗa da:

Samar da jam'iyya fiye da ɗaya : Farfesa Kari ya ce a tsarin mulki irin na siyasa mutane na da damar kafa jam'iyyunsu, waɗanda da su ne za su tsaya takarar kowane irin matsayi, da gwagwarmayar neman madafun iko domin su gusar da abubuwan ƙi a cikin al'umma, su kuma bijiro da abubuwan alƙairi a cikin al'umma,.

Ana son kuma samar da jam'iyya fiye da ɗaya, ta yadda idan an zo batun warware wata matsala, idan wasu suka ce a yi hagu, za a samu wadanda za su ce a yi dama, daga bab sai a cma matsaya, in ji Dakta Dukawa.

Zaɓe: Farfesa Abubakar Kari ya ce siyasa wani tsari ne da ya yardar wa al'ummar su zaɓar wa kansu shugabannin da za su jagorance su, waɗanda suke so, ba wai a yi musu ƙarfa-ƙarfa ba.

Dakta Sa'idu Dukawa kuwa cewa ya yi ta hanyar waɗanna jam'iyyu mutane da dama za su tsaya takara su kuma bayyana wa al'umma manufofinsu da za su sa mutane su yi imani da su domin zaɓarsu.

Damar taka rawa: Farfesa Kari ya kuma ce siyasa wata aba ce da ke bayar da dama ga mutane su taka rawa ta fuskar tsayawa takara domin a zaɓe su, ko kuma su za bi wanda zai jagorance su.

''Damar gudanar da za be na daga cikin manyan ginshiƙar na dimokraɗiyya'', in ji Farfesa Kari

Chanjin Gwamnati : Wata siffa da siyasa ke da ita, ita ce ta sauyin gwamnati, akan ƙayyadewa shugabannin wa'afdin mulki a tsarin siyasa, ta yadda al'umma za su samu damar canja gwamnatin da ke mulkarsu idan ba su gamsu da irin rawar da take takawa ba, ko kuma suna buƙatar sauyi, kamar yadda Dakta Dukawa ya yi bayani.

''Hakan zai sa a riƙa samun sauyin gwamnati cikin lumana ba tare da an zubar da jini ba, wanda ya faɗi zaɓe yana haƙura cewa an kayar da shi, wanda ya yi nasara ba zai danne wanda ya faɗi ba, to shikenan an samu tsarin siyasar dimokraɗiyya mai kyau '', in ji Malamin jami'ar.

Mulki bisa doron tsarin mulki: Siyasa na nufin gudanar da mulki bisa kundin tsarin mulkin ƙasa, wato ba mutum ɗaya ba ne ko wasu tsirarun mutane za su riƙa yin abin da suka ga dama, in ji Farfesa Kari.

Mene ne mafita?

Dakta Dukawa ya ce akwai hanyoyi da za a bi wajen kyautata tunanin da talakawa ke yi wa 'yan siyasa musamman a Najeriya, hanya ta farko ita ce:

Samun ilimin siyasar: Ya ce ya kamata duk mutumin da ke da sha'awar shiga siyasa ya daure ya nemi ilimin siyasar.

''Ko dai a aji ko a soron waɗanda suke 'yan siyasar ne, waɗanda sun yi ta a aikace, ya nemi iliminta.

Tsarkake niyya: Yana da kyau duk wanda zai shiga siyasa ya tsarkake niyyarsa, in ji malamin siyasar.

''Kar ya shiga da niyyar ya more wa wasu alfarmomi da ake samu a shugabanci, ana so a shiga siyasa ne don an hango wata matsala da ta addabi al'umma kuma mutum yana ganin yana da fikirar yadda zai warware wannan matsalar.

Farfesa Kari ya ce ya kamata tun daga kafa jam'iyyun siyasa a riƙa tsarkake niyyar cewa an kafa su ne da nufin ciyar da ƙasa gaba

Masu ilimin siyasa su riƙa shiga: Yana da kyau masu ilimin siyasa da yawa su riƙa shiga siyasar, domin ta haka ne za a iya magance duka matsaolin da ke tattare da ita

Yin aiki tuƙuru: Farfesa Kari ya ce abin da ya kamata 'yan siyasa su siffantu da shi, shi ne yin aiki tuƙuru wajen hidimta wa al'umma, kar su bai wa maraɗa kunya.

''Su tsaya su bauta wa al'umma, kada su riƙa amfani da siyasa a matsayin hanyoyin samun mulki da arzuta kai da biya kai buƙatu, a maimakon haka su riƙa saka buƙatun al'umma a sahun farko'', in ji Farfesa Kaeri.

Ya ce babbar matsalar da ake samu a Najeriya ita ce, idan aka samu dan siyasa na gari guda ɗaya ya shiga siyasa to sai an samu ɓata-gari fiye da 100 da suka shigeta, wanda hakan kuma zai sa ba zai iya yin wani tasiri wajen kyautata siyasar ƙasar ba, kasancewar shi kaɗai ne.

Farfesa Abubakar Kari ya ce muddin 'yan siyasa suka siffantu da waɗannan siffofi to tabbas za sauya yadda mutane ke kallon siyasa a yanzu, zuwa wani abu mai kyau.