Abin da ya kamata ku sani kan wasan Betis da United a Europa

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Betis za ta kara da Manchester United a Europa League ranar Alhamis a Sifaniya.

Wasa na biyu kenan da za su buga a bana a zayaen 'yan 16 a gasar ta zakarun Turai, kuma karo na biyu da za su kece raini a tsakaninsu a tarihi.

Ranar 9 ga watan Maris United ta doke Real Betis da cin 4-1 a Old Trafford, kuma ta ci kwallo ta hannun Marcus Rashford a minti shida da fara wasa.

Tun kan hutu Betis ta zare ta hannun Ayoze Perez, bayan da suka koma zagaye na biyu ne United ta kara ta hannun Antony, sai Bruno Fernandes ya ci na uku, sannan Wout Weghorst ya zura na hudu a raga

Sai dai Manchester United za ta buga wasa na biyu a Sifaniya ba tare da Antony ba a gasar ta Europa League.

Mai shekara 23 bai yi atisaye ba ranar Laraba, saboda rashin lafiya, United ba ta je da shi Sifaniya ba daga 'yan wasa 21 da ta bayyana.

Kociyan United, Erik ten Hag ya ce Casemiro da Bruno Fernandes za su buga masa wasan, duk da cewar saura kati daya na gargadi da kowanne zai karba a dakatar da shi wasan gaba.

Haka kuma United za ta fafata ba tare da Anthony Martial ba, wanda ya dade yana jinya da Donny van de Beek da Christian Eriksen da kuma Alejandro Garnacho.

United wadda ta dauki Carabao Cup a bana tana buga FA Cup, bayan da take fatan kai wa daf da na kusa da na karshe a Europa League.

Haka kuma kungiyar Old Trafford tana ta uku a Premier League a kakar nan, wadda ke fatan ta kare a 'yan hudun farko ko ta buga Champions League a badi.

United ta taba lashe Europa League a kakar 2016/17 karkashin Jose Mourinho, wanda ya dauki League Cup a dai kakar.

Ita kuwa Real Betis ba ta taba daukar kofin na zakarun Turai na Europa League ba.