PSG ta kammala daukar Nordi Mukiele daga RB Leipzig

An wallafa

Paris St-Germain ta kammala sayen mai tsaron baya, Nordi Mukiele daga RB Leipzig kan yarjejeniyar kaka biyar.

Dan kwallon tawagar Faransa ya yi kaka hudu yana taka leda a Jamus, bayan da ya koma can daga Montpellier,.

Ya kuma taimaka da Leipzig ta kai karawar daf da karshe a Europa League da kuma daukar German Cup a kakar da ta wuce..

Ya buga wasa 145 a kungiyar da ke buga Bundesliga da cin kwallo 10 da bayar da 11 aka zura a raga.

A can baya Chelsea ta yi sha'awar daukar dan wasan mai shekara 24.

Mukiele ya wakilci tawagar Faransa ta matasa 'yan kasa da shekara 18, wadda ya fara yi mata wasan cikin Satumbar 2021 a karawa da Finland a neman shiga gasar kofin duniya.

Mai tsaron baya daga gefen hagu, wanda ke iya tsaron baya daga tsakiya shi ne na uku da PSG ta dauka a bana.

PSG ta dauki aron Hugo Ekitike daga Reims da kuma Vitinha daga Porto kan kwantiragi kaka biyar.

Shi ne na biyu da ya koma PSG tun bayan da sabon koci, Christophe Galtier ya karbi daga hannun Mauricio Pochettino a karshen kakar da aka karkare.