Nicolas Pepe na Arsenal zai koma taka leda aro a Nice

An wallafa

Kungiyar da ke buga gasar Ligue 1 a Faransa, Nice na tattaunawa da Arsenal, domin daukar aron Nicolas Pepe.

BBC ta fahimci cewar cikin kunshin yarjejeniyar ba batun sayar da dan wasan mai shekara 27 ga kungiyar, wanda ya yi wa Gunners karawa biyar a bara.

Pepe ya koma taka leda a Arsenal a matakin wanda ta dauka mafi tsada a tarihin kungiyar kan fan miliyan 72 a 2019, amma ya kasa nuna kwarewarsa a gasar Premier League.

Dan kwallon tawagar Ivory Coast, wanda bai buga wasa ko daya ba a kakar nan, yana da sauran kwantiragin da zai kare a 2024.

Mikel Arteta ya kara karfin Arsenal a kakar nan, wanda ya dauki Gabriel Jesus da Fabio Vieira da matashi dan kasar Brazil, Marquinhos.

Ana kuma alakanta Arsenal da cewar tana son daukar dan kwallon tawagar Wolverhampton, Pedro Neto kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai a bana.