Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United ta kammala daukar Tyrell Malacia daga Fayenoord
An wallafa
Manchester United ta kammala daukar Tyrell Malacia kan fam miliyan 13 daga Feyenoord, kan yarjejeniyar kaka hudu.
Kenan kwantiragin dan wasan zai kare a karshen watan Yunin 2026, za kuma a iya tsawaitawa kaka daya.
Dan kwallon tawagar Netherlands, mai tsaron baya ya buga wasa 136 a Feyenoord, kungiyar da ya fara tun yana matashi.
Malacia, mai shekara 22, ya zama na farko da Erik Ten Hag ya dauka a matakin sabon kociyan United a bana.
Dan wasan na tattaunawa da kungiyar Faransa, Lyon daga baya United ta shiga cinikin da ta kai ta mallaki dan kwallon.