Brighton ta caskara Chelsea a wasan da Potter ya ziyarci Amex

Brighton vs Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Brighton ta ci Chelsea 4-1 a wasan mako na 14 a gasar Premier League da suka fafata ranar Asabar.

Karon farko da Graham Potter ya ziyarci Amex, bayan da ya bar Brighton ya karbi aikin horar da Chelsea a cikin watan Satumba.

Minti na biyar da fara wasa Leandro Trossard ya fara cin kwallo, daga baya Chelsea ta ci gida ta hannun Ruben Loftus-Cheek da kuma ta hannun Trevoh Chalobah.

Haka aka je hutu Brighton da cin kwallo uku, Chelsea na nema - karo na uku da Brighton ta zura uku a raga tun kan hutu, inda biyun a karkashin Graham Poter ne.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Kai Havertz ya zare daya, sannan Brighton ta kara na hudu ta hannun Pascal Gross.

Chelsea ta yi rashin nasara ne, bayan yin wasa shida a Premier ba a doke ta ba har da canjaras biyu daga ciki - ko a baya duk lokacin da kungiyar Stamford Bridge ta yi wannan kwazon a kan doke ta a karawar gaba.

Wannan nasarar ta zama ta 100 da Brighton ta yi a Premier League.

Kafin wannan fafatawar Brighton ta fuskanci kungiyoyi 109 duk ta doke su, in banda Chelsea, sai a wannan karon ta yi nasara a kan kungiyar Stamford Bridge.

Wannan shi ne karon farko da aka doke Potter a wasa na 10 da ya ja ragamr Chelsea da cin shida, tun bayan da ya maye gurbin Thomas Tuchel.

Brighton za ta buga wasan gaba a Premier League da Wolverhampton, ita kuwa Chelsea Champions League za ta kara da Dinamo Zagreb.