Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Girona ta koma ta biyu a teburin La Liga da maki iri daya da na Real
Girona ta koma ta biyu a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Almeria 5-2 a wasan La Liga karawar mako na 10 ranar Lahadi.
Minti biyu da take leda Almeria ta fara zura kwallo ta hannun Leo Baptistao, sannan ya kara na biyu a minti na 22 tsakani.
Tun kan hutu Girona ta farke biyun ta kara na uku ta hannun Ivan Martin Nunez da Artem Dovbyk, wanda ya kara na uku na biyu a wasan.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Olivo Moreira de Oliveira ya ci na hutu, sannan Cristhian Stuani ya kara na biyar a raga.
Da wannan sakamakon Girona, wadda ke taka rawar gani a kakar bana tana ta biyun teburin La Liga da maki 25 iri daya da na Real Madrid, bayan mako 10.
Ranar Asabar Real Madrid ta tashi 1-1 a gidan Sevilla, hakan ne ya bai wa Girona damar samun hawa kan mataki na biyun.
Har yanzu Almeria ba ta samu ta ci wasa ba a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, wadda aka yi fafatawar mako na 10.
A ranar Asabar Atletico Madrid ta dare mataki na biyu a teburin La Liga, bayan da ta doke Celta Vigo 3-0, kuma Antoine Griezmann ya ci uku rigis.
Watakila Barcelona ta koma mataki na uku, wadda za ta karbi bakuncin Athletic Bilbao, idan ta yi nasara a karawar.