Bellingham ya ci Man United a wasan da Real Madrid ta yi nasara 2-0

Jude Bellingham

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta doke Manchester United 2-0 a wasan sada zumunta don gwada 'yan wasan da za su buga kakar bana da za a fara cikin watan Agusta.

Manyan kungiyoyin Turan biyu sun kara ne a Houston din Amurka, inda suka baje 'yan kwallonsu a gaban dubban magoya bayansu.

Minti shida da fara sa wasa Jude Bellingham ya ci United da ya zura a raga a matakin sabon dan kwallon Real Madrid a wasa na biyu da ya buga mata.

Saura minti daya a shiga karin lokaci ne Real ta kara na biyu ta hannun Joselu.

Bellingham dan kwallon tawagar Ingila, shi ne aka zaba mafi kwazo a karawar.

Mai shekara 20 ya koma taka leda Real Madrid a bana daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 88.5.

United ta yi amfani da sabon mai tsaron raga, Andre Onana a wasan, wanda ta dauko daga Inter Milan, bayan da David de Gea ya bar kungiyar a karshen kakar da ta wuce.

An buga wasan ne a NRG Stadium mai cin 'yan kallo 67,801.