Yadda yaro ɗan makaranta mai kunya ya zama shugaban ƙasa

An wallafa

Daga Omega Rakotomalala da Farouk Chothia a Nairobi da London

Traore

Asalin hoton, Reuters

Yaron da aka sani da kunya amma kuma mai matuƙar basira, wato Kyaftin Ibrahim Traoré ya zama shugaban ƙasa na mulkin soji da ya ƙwace iko a wani juyin mulki a baya-bayan nan a Burkina Faso da ya ke yankin Afirka ta Yamma.

Ya yi wa tsohon ubangidansa Laftanal Kanal Paul-Henri Damiba juyin mulki ranar 30 ga watan Satumba, bayan zarginsa da gaza cika alkawarinsa na magance matsalar masu tayar da ƙayar baya da ke addabar ƙasar tun shekarar 2015.

Matashin mai shekara 34 wanda aka haifa a shekarar 1988, ya zama shugaban ƙasa mafi yarinta a Afirka, inda ya shiga sahun wasu jagororin juyin mulkin - da Kanal Mamady Doumbouya na Guinea da aka haifa a 1981, da kuma na Mali Kanal Assimi Goïta, da aka haifa a 1983.

"Na san da yawan ku a nan kun girme ni. Ba mu so abin da ya faru ya faru ba, amma kuma ba mu da zaɓi," kamar yadda Kyaftin Traoré ya shaida wa jami'an gwamnati.

A lokacin ɗan gajeren mulkin Laftanal Kanal Damiba, an samu ƙaruwar hare-haren da ke da alaƙa da masu tsattsauran ra'ayin Islama da kuma al-Qaeda a Burkina Faso, kuma sun ƙwace yankuna a karkara suka kuma zagaye birane, inda gwamnati ta zama tana da iko da kashi 60 cikin 100 kawai na ƙasar, a cewar wani ƙiyasi.

A ƙasar da babu wani ƙwaƙƙwaran tushe na dimokradiyya a ƙasar da tuni sojoji suka mamaye ta, Kyaftin Traoré ya ƙwace mulki da alkwarin inganta tsaro a ƙasar da ke cikin tsoron masu tayar da ƙayar baya.

Juyin mulkin nasa - wanda shi ne na biyu da aka yi a Burkina Faso cikin ƙasa da wata tara - shi ne alamu na baya-baya da ke nuna cewa akwai guguwar juyin mulki kamar yadda shugaban Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, ya nuna damuwa akai a 2021.

"Roƙona, musamman ga manyan ƙasashen duniya - shi ne a haɗa hannu don haɗin kan Kwamitin Tsaro don tabbatar da cewa an shawo kan wannan guguwa ta juyin mulki," a cewar Mr Guterres a lokacin da abin ya faru.

Amma a lokacin da manyan ƙasashen duniya ke fuskantar nasu matsalolin - da kuma yaƙin Ukraine - sun ƙi mayar da hankali sosai kan rashin tabbas din da ake ciki a ƙasashen da ake fama da juyin mulki irin su Burkina Faso.

Burkina Faso da sauran ƙsashe sun samu kansu a cikin yaƙin cacar baka da adawar da ta samu sakamakon yakin Ukraine, a yayin da Rasha ke faɗaɗa ikonta a yankin don yi wa Faransa fintinkai, wacce take da alaƙa da ƙut-da-ƙut ta tattalin arziki da soji da ƙasashen da ta raina ɗin.

Capt Ibrahim Traoré has promised to improve security in Burkina Faso

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kyaftin Ibrahim Traoré ya yi alkawarin inganta tsaro a Burkina Faso
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Na san cewa Faransa ba za ta iya shiga huruminmu kai tsaye ba," a cewar Kyaftin Traoré, yana mai cewa: "Amurka ce abokiyar hulɗarmu a yanzu."

Kalamansa na nuna cewa zai iya bin sahun takwaransa na Mali, wanda ake zargi da jawo ce-ce-ku-ce kan ƙungiyar tsaro ta Rasha, Wagner, don maye gurbin Faransa a yaƙin da take yi da ta'addanci.

Kyaftin Traoré ya soma aikinsa ne da yaƙi da masu ikirarin jihadi a Mali.

Ya yi aiki a rundunar sojin MDD, an kuma ce ya sha nuna gwarzantaka a yayin wasu munanan hare-hare da masu tayar da ƙayar baya suka kai a yankin Timbuktu da ke arewacin ƙasar a 2018.

A shekarar da ta biyo baya, ya yi aiki a yankin Otapuanu na Burkina Faso har tsawon wata bakwai.

Ya kuma yi aiki a yankin Markoye da arewacin yankin Sahel inda ya fafata sosai.

"Traore yana da alaƙa ta ƙut da jami'ansa, yana da ƙwazo da jarumtaka. BA ya iya wata shaida ba tare da ya je filin daga ba," a cewar wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunanta.

Sai dai Kyaftin Traore bai kai muƙamin janar din soja ba, kyaftin ne shi da ya yi karatunsa a wata makarantar soji, ya kuma fara aikin sojin a shekarar 2009, sannan ya samu horo sosai a Moroko.

Ya zabi shiga soji ne bayan kammala karatunsa na sakandare a birni na biyu mafi girma a Burkina Faso wato Bobo-Dioulasso, inda rahotanni suka bayyana shi a matsayin "mai kunya" amma kuma "mai basira."

A yanzu Kyaftin Traoré ya samu kansa a yanayin da idon duniya zai koma kansa, inda har wasu suka fara kwatanta shi da tsohon fitaccen shugaban ƙasar Thomas Sankara.