Yadda wata mata ta zargi likitoci da cire mata ƙoda a asibitin Gombe

    • Marubuci, Abubakar Maccido
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wata mata mai juna biyu ta ce ta je asibiti da sassan jikinta lafiya, amma bayan an yi mata tiyatar haihuwa ta hanyar CS, sai ta gano cewa an cire mata ƙoda ɗaya.

Barira Alhassan, mace mai matsakaicin shekaru daga jihar Gombe, ta zargi likitocin Asibitin Ƙwararru na jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya da cire mata ƙoda ɗaya yayin da suke yi mata tiyatar haihuwa.

Sai dai mahukuntan asibitin sun musanta wannan zargi. A cikin wata sanarwa, asibitin ya bayyana zargin a matsayin "ƙarya tsagwaronta, mara tushe kuma babu wasu gamsassun hujjojin, ko bayanan asibiti da kuma bayanan mara lafiyar."

Ƴan uwanta sun ce, sakamakon gwaje-gwajen lafiya da aka yi mata kafin tiyatar ya nuna cewa tana da ƙodoji biyu cikin ƙoshin lafiya, amma bayan tiyatar, ta kamu da rashin lafiya mai tsanani, inda wasu gwaje-gwajen da aka sake yi suka nuna cewa yanzu tana da ƙoda ɗaya ce kawai.

A hirarta da BBC, Barira Alhassan ta ce an yi mata tiyatar ne a ranar 8 ga watan Afrilun 2026, kuma bayan ƴan kwanaki kaɗan ta fara fama da rashin lafiya.

"Bayan ƴan kwanaki da yi min tiyata, sai na fara rashin lafiya sosai. Ina amai, cikina yana ciwo sosai, jikina ya kumbura, sannan duk lokacin da zan yi fitsari ina jin zafi," in ji ta.

Ta ƙara da cewa: "Sai na fara tambayar wasu mata da aka taɓa yi wa tiyatar CS ko su ma haka suka ji bayan an yi musu aiki, domin wannan shi ne karo na farko da aka yi min tiyata duk da cewa na haifi ƴaƴa goma."

Barira ta ce wani likita ne da ya fara duba lafiyarta ya sanar da ita cewa yanzu tana da ƙoda ɗaya ne kawai, lamarin da ya ba ta matuƙar mamaki.

"Na shiga cikin tashin hankali lokacin da likitan ya ce min ina da ƙoda ɗaya kawai. Har ma ya tambaye ni ko na sayar da ita ne".

"Na ce masa a'a. Daga nan sai ya fara kwantar min da hankali, yana cewa mutum na iya rayuwa da ƙoda ɗaya kamar kowa. Daga baya ya ba ni magunguna," in ji Barira.

Ta ƙara da cewa bayan da ƴan'uwanta suka nace sai an bayyana musu abin da ya faru, sai take ganin kamar mahukuntan asibitin na ƙoƙarin shawo kansu kada lamarin ya fito fili.

"Yanzu da muka nace cewa sai an gaya mana abin da ya faru, sai muka ga kamar asibitin na ƙoƙarin rarrashinmu ne domin kada maganar ta fito fili," in ji Barira.

Bayan samun wannan bayani, iyalan Barira sun kai ƙorafi ga mahukuntan Asibitin Kwararru na Gombe, inda suka nemi bayanan lafiyarta daga asibitin, sai dai an shaida musu cewa ba a samu kundin bayananta ba.

Ɗan'uwanta, Zakari Alhassan, ya shaida wa BBC cewa sun kai ƙorafin ne saboda wani hoton gwajin lafiya (scan) da aka yi wa Barira tun a shekarar 2015 ya nuna tana da ƙododi biyu masu lafiya.

Zakariyya Alhassan ya ce, mahaifinsu ya je asibitin domin neman bayani kan abin da ya faru, amma bai samu gamsasshiyar amsa ba.

"Mahaifinmu ya je asibitin domin ya san abin da ya faru, amma ba a ba shi wani gamsasshen bayani ba. Ya ce abin da yake son sani shi ne abin da ya faru da ƙodar ƴarsa da ta ɓace," in ji Zakariyya.

Ya ƙara da cewa asibitin ya ce ba su samu kundin bayanan Barira ba, duk da cewa ta saba zuwa asibitin kuma a nan ne ta haihu.

"Wannan ya ƙara mana damuwa tare da ƙarfafa mana zargin cewa akwai wani abu da aka yi wa ƴar uwarmu."

Iyalan Barira sun ce sun gabatar da ƙorafe-ƙorafe da dama, amma har yanzu ba su samu amsar da ta gamsar da su ba.

Zakariyya ya ce da ya ga babu wani ci gaba, sai ya rubuta takardar ƙorafi zuwa Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Gombe, yana neman adalci da kuma a gudanar da bincike kan lamarin.

"Daga baya na rubuta takardar ƙorafi ina neman adalci da kuma bincike. Bayan haka, ma'aikatar ta gayyaci ƴar'uwata da mijinta da kuma ma'aikatan asibitin, inda ta buƙace mu kada mu fito da batun a bainar jama'a har sai an kammala binciken."

Sai dai Zakariyya ya ce har yanzu ba su gamsu da yadda ake tafiyar da lamarin ba, don haka iyalan na ci gaba da neman a gudanar da cikakken bincike.

Ita ma Barira ta ce abin da take so shi ne a yi mata adalci.

"Abin da nake so shi ne a gudanar da cikakken bincike domin a bayyana yadda na rasa ƙodata, sannan a yi min adalci," in ji ta.

Asibitin ya musanta zargin cire mata ƙoda

Mahukuntan Asibitin Kwararru na Jihar Gombe sun musanta zargin cewa wani likita a asibitin ya cire wa Barira Alhassan ɗaya daga cikin ƙodojinta yayin da ake yi mata tiyatar haihuwa.

A cikin wata sanarwa, asibitin ya bayyana zargin a matsayin "ƙarya tsagwaronta, mara tushe kuma babu wasu gamsassun hujjojin, ko bayanan asibiti da kuma bayanan mara lafiyar."

Asibitin ya ce bayanan ɗakin tiyata sun nuna cewa an yi wa Barira tiyatar haihuwa ta gaggawa (Emergency CS) ne kawai, ba tare da an yi mata wata tiyata da ta shafi ƙodojinta ba.

"Babu inda bayanai suka nuna likitocin da suka yi mata tiyatar sun taɓa wani abu da ya shafi ƙodojinta," in ji mahukuntan asibitin.

Asibitin ya ce bayan iyalan Barira sun nuna damuwa kan lamarin, an gudanar da ƙarin bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.

A cewar sanarwar, wani gwajin da aka yi a wani Asibitin Koyarwa na Tarayya ya nuna sakamakon da ke nuni da cewa wataƙila Barira ta zo duniya ne da ƙoda ɗaya, ba wai ta rasa ƙodar ne sakamakon tiyatar ba.

Asibitin ya kuma ce shi ne ya biya kuɗin wannan gwaji domin a tabbatar da gaskiya.

"Yana da kyau a gane cewa mahukuntan asibitinmu ne suka biya kuɗin wannan bincike, domin taimakawa wajen gano gaskiyar lamarin," in ji sanarwar.

Mahukuntan asibitin sun ce sun gana da Barira da iyalanta sau biyu, inda suka yi musu bayani kan sakamakon binciken tare da duba dukkan bayanan lafiyarta.

Sanarwar ta ƙara da cewa daga baya iyalan Barira sun buƙaci a sake yin binciken a wata cibiyar lafiya mai zaman kanta, kuma asibitin ya amince da hakan.

"A halin yanzu, mahukuntan asibitin na jiran iyalan su gabatar da sakamakon sabon binciken kamar yadda aka cimma yarjejeniya a taronmu na ƙarshe," in ji sanarwar.

Asibitin ya kuma yi zargin cewa yaɗa wannan batu a kafafen sada zumunta ɓata suna ne kawai da kuma rage amincewar jama'a da ma'aikatan lafiya.

Sai dai ya jaddada cewa ba a cire wa Barira wata ƙoda ba yayin tiyatar da aka yi mata.