Chelsea da West Ham na son Duran, Musiala na son zuwa Premier

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea da West Ham na daga cikin ƙungiyoyin da ke sa ido sosai a kan ɗan wasan gaba mai kai hari na Aston Villa Jhon Duran, mai shekara 20, ɗan Kolombiya. (Give Me Sport)
Ba tare da son ranta ba Nottingham Forest za ta sayar da Murillo idan ta samu tayi mai girma a kan ɗan bayan nata na Brazil, mai shekara 22, wanda ake dangantawa da tafiya Barcelona da Real Madrid. (Football Insider)
Ɗan wasan gaba na gefe na Jamus Jamal Musiala, mai shekara 21, wanda sai a 2026 kwantiraginsa da Bayern Munich zai ƙare ya ce, a shirye yake da komai amma kuma ya ƙara da cewa yana jin daɗi a ƙungiyar da yake, yayin da ake maganganu cewa wata rana zai iya tafiya gasar Premier. (Guardian)
Ɗan wasan gaba na gefe na Villarreal Alex Baena, na Sifaniya, mai shekara 23, ya ɗauki hankalin masu nema wa Aston Villa da Newcastle United 'yan wasa a bana. (Caught Offside)
Shugabannin Bayern Munich sun yi amanna cewa sun sayi tauraron ɗan wasan da kuɗinsa ya kai fam miliyan 100, a rabin farashin lokacin da suka kasa Manchester United a sayen Michael Olise, na Faransa mai shekara 22, a kan fam miliyan 50, daga Crystal Palace. (Mirror)
Wataƙila Southampton ta karkata wajen tsohon kociyan Chelsea da Brighton Graham Potter idan ta yanke shawarar sallamar Russell Martin. (Football Insider)
Ɗan wasan gaba na gefe na Ingila Eberechi Eze ba shi da wata matsala kan wajen da yake taka leda a Crystal Palace, ƙungiyar da take mamakin cewa ba ta samu ƙarin buƙatar sayen ɗan wasan ba daga manyan ƙungiyoyin Premier a lokacin bazara. (Mirror)
A shirye Newcastle United take ta bar ɗan wasan gaba na gefe na Ingila Callum Wilson, mai shekara 32, ya bar ƙungiyar ba tare da wani kwantiragi a kansa ba a bazara mai zuwa idan ba su sami wanda zai maye gurbinsa ba a watan Janairu. (Give Me Sport)
Ɗan wasan gaba na Turkiyya Yusuf Yazici, mai shekara 27, na shirin sanya hannu a kwantiragin shekara uku da Olympiakos ta Girka, bayan barin Lille ta Faransa. (Fabrizio Romano)










