Arsenal da Man Utd da Chelsea na rububin Schick, Tsimikas zai bar Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta yi tayin sayen Liam Delap, Gunners na fatan tsawaita kwantiragin William Saliba, makomar Emiliano Martinez a Aston Villa na iya zama cikin shakku.
Arsenal ta yi tayi ga wakilan dan wasan gaba na Ipswich Liam Delap, mai shekara 22, yayin da suke neman siyan gogaggen dan wasan gaba gwanin cika aiki da ya yi, kuma aka gani a kasa. (Football Transfers)
Haka kuma Gunners din sun kara matsa kaimi don tsawaita kwantiragin dan wasan bayan Faransa William Saliba, wanda ake alakanta shi da Real Madrid. Manufar ita ce a hana dan wasan mai shekaru 24 tashi a farashi mai sauku yayin da ya rage shekara guda kwantiraginsa ya kare a bazara mai zuwa, ko kuma ya tashi a kyauta idan kwantaraginsa ya kare a 2027. (L'Equipe)
Makomar golan Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 32, a Aston Villa na iya zama cikin shakku, yayin da kulob din ke son siyan sabon mai tsaron gida a kasuwar musayar 'yan wasa ta bazara. (Mail)
Liverpool a shirye take ta siyar da dan wasan baya na kasar Girka Kostas Tsimikas mai shekara 28 a bazara. (Football Insider)
Arsenal da Manchester United da Chelsea duk suna zawarcin dan wasan Bayer Leverkusen na Jamhuriyar Czech, Patrik Schick, mai shekara 29 a bazara. (Cought Offside)
Chelsea da Liverpool ne ke kan gaba wajen zawarcin dan wasan bayan Bournemouth da Spain Dean Huijsen, mai shekara 20. (Teamtalk)
Al-Hilal na jiran amsa daga kocin Inter Milan Simone Inzaghi da take son ya zama kocinta, kuma idan ya ki amincewa da su, kungiyar Saudi Pro League za ta iya daukar kocin Fulham Marco Silva. (Talksport)
Mai kungiyar Napoli Aurelio de Laurentiis ya kara tuntubar tsohon kocin Juventus da AC Milan Massimiliano Allegri don daukarsa, idan koci Antonio Conte ya bar kungiyar a karshen kakar wasa ta bana. (Tutomercatoweb)
Manchester United na zawarcin dan wasan Italiya da Fiorentina Moise Kean mai shekaru 25. (Footmercato)










