Mun lashe Firimiya biyu a kaka biyu da suka gabata - Arteta

Mikel Arteta

Asalin hoton, PA Media

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Mikel Arteta cikin raha ya yi ikirarin cewa Arsenal ta lashe kofin Firimiya sau biyu saboda sun samu maki fiye da na Liverpool da ya ba ta damar lashe kofin gasar a bana.

Arteta na nufin cewa Liverpool ta lashe kofin Firimiya da makin da bai kai na Arsenal ba a kaka biyu da take ƙarewa ta biyu bayan Manchester City.

"Lashe kofuna na nufin kasancewa cikin lokacin da ya dace. Liverpool ta lashe kofin da makin da bai kai namu ba a kaka biyu. Idan aka yi la'akari da yawan makinmu a kaka biyu, zai zama mun lashe kofin Firimiya sau biyu kenan," kamar yadda kocin na Arsenal ya bayyana cikin murmushi.

Sai dai Liverpool ta lashe kofin Firimiya ne yayin da ya rage wasa uku a kammala gasar, kuma za ta iya samun maki fiye da na Arsenal 89 a kakar da ta gabata, kuma ta yi kankan da makin da Arsenal ta samu a kakar 2022-23.

Liverpool ta ba Arsenal da ke matsayi na biyu tazarar maki 15, tazarar maki uku da Manchester City da ke matsayi na uku, bayan ta sha kashi a hannun Bournemouth.

Arsenal za ta haɗu da Liverpool a Anfield a ranar Lahadi.

Arsenal na iya kawo ƙarshen fatarar kofin da take yi idan har ta iya doke Paris St-Germain a karawar da za su yi a gasar Zakarun Turai.

Inter Milan ce ke jiran Arsenal ko PSG a wasan ƙarshe a Zakarun Turai bayan doke Barcelona jimillar kwallaye 7-6 a wasan dab da ƙarshe.