Man United na sha'awar ɗaukar Cunha daga Wolves

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United na sha'awar ɗaukar ɗan wasan Wolverhampton, Matheus Cunha a karshen kakar nan.

Ɗan kasar Brazil, wanda aka gindaya £62.5m idan kwantiraginsa bai kare ba ga mai son sayen shi, yarjejeniyarsa za ta kare a Molineux da zarar an kammala kakar nan.

Wasu rahotanni da yawa sun sanar da BBC cewar Cunha, mai shekara 25 yana daga cikin waɗan da United ke fatan ɗauka har da Liam Delap, mai shekara 22 na Ipswich Town.

United na fatan kara karfi a gurbin cin ƙwallaye, wadda ta zura 33 a raga a Premier League, inda Southampton da Leicester City da Ipswich da Everton da kuma West Ham ne suke da karancin cin ƙwallaye da bai kai yawan na United ba.

Ruben Amorin na hangen Cunha zai taka rawar gani a gurbin mai cin ƙwallo a irin salon da yake jan ragamar United na 3-4-2-1.

Cunha, wanda shi ne kan gaba a yawan ci wa Wolves ƙwallaye mai 16 a bana a dukkan fafatawa, yana bayar da gudunmuwa karkashin, Vitor Pereira.

United za ta yi takara wajen sayen Cunha daga manyan ƙungiyoyin Premier League da ya haɗa da Liverpool da Arsenal da Chelsea da kuma Newcastle United.

Cunha ya zura ƙwallo 32 a raga a wasa 87 da ya buga wa Wolves, to amma rashin ɗa'a da yake a lokacin taka leda, zai zama abin damuwa ga kowacce ƙungiya da ke son sayen shi.

Cunha tsohon ɗan wasan Atletico Madrid ya karɓi jan kati biyu a bana, hakan ya sa aka dakatar da shi wasa shida.