Man City ta kasa doke Southampton a Premier League

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Southampton da Manchester City sun tashi 0-0 a wasan mako na 36 a Premier League da suka kara ranar Asabar a filin wasa na St Mary.

Da City wadda take ta ukun teburin kakar bana ta ci wasan da ta haɗa maki iri ɗaya da na Arsenal ta biyu mai 67, yanzu tana ta 65, saura wasa biyu a gabanta.

Ƙungiyar Etihad ta buga karawar ce mako ɗaya tsakani kan ta fuskanci Crystal Palace a wasan karshe a FA Cup da za su kara a Wembley.

Wannan shi ne kofin da ya rage a gaban City, mai rike da Premier League na bara, idan ba haka ba za ta kare kakar nan ba tare da lashe kofi ba.

City mai fatan samun gurbin Champions League a baɗi tana da tazarar maki biyu tsakaninta da Newcastle ta huɗu da kuma Chelsea ta biyar masu maki 63 kowacce.

Ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama ce ta mamaye wasan, amma ta kasa zura ƙwallo a ragar Southampton wadda aka ɗurawa 82 kawo yanzu.

Kenan City ta kasa cin ƙwallo a karawa huɗu daga wasa 11 baya a Premier League a kakar bana.

Ƙungiya biyar ce za ta wakilci Ingila a Champions League kai tsaye a baɗi, yayin da duk wadda ta lashe Europa League tsakanin Tottenham da Manchester United, itama za ta je gasar zakarun Turai a badi.

Tuni dai Southampton ta faɗi daga Premier League zuwa Championship a baɗi, wadda ita ce ta karshen teburi - sauran da suka bi bayanta sun haɗa da Ipswich Town da kuma Leicester City.

Sauran wasannin da suka rage a gaban Man City a bana:

FA Cup ranar Asabar 17 ga watan Mayu

  • Crystal Palace da Man City

Premier League Talata 20 ga watan Mayu

  • Man City da Bournemouth

Premier League Ranar Lahadi 25 ga watan Mayu

  • Fulham da Man City