Chelsea na yin cefane a bana amma miyar ba ta fara dadi ba

Thomas Tuchel

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kungiyar Chelsea ta sha kashi da ci 3-0 a hannun Leeds United ranar Lahadi a wasan mako na uku a gasar Premier League a Elland Road.

Kawo yanzu Chelsea tana ta 12 a teburin kakar bana da maki hudu, bayan cin wasa daya da canjaras daya daga karawa ukun da ta yi.

Chelsea ta fara da cin Everton 1-0 a wasan makon farko a Goodison Park, sannan ta tashi 2-2 da Tottenham a wasan hamayya a Stamford Bridge.

An fara sa shakku kan rawar da Chelsea za ta taka a kakar nan, bayan cefanen sama da fam miliyan 170 da ta yi a kakar nan.

Tuchel na son kara karfin kungiyar kan a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta bana.

Kungiyar na zawarcin mai tsaron bayan Leicester, Wesley Fofana, bayan da ta dauki 'yan wasa shida kawo yanzu.

Jerin 'yan wasan da Chelsea ta dauka a bana

Raheem Sterling

Asalin hoton, Getty Images

Raheem Sterling (fam miliyan 50 daga Manchester City)

Kalidou Koulibaly (fam miliyan 34.2 daga Napoli)

Omari Hutchinson (Kwantiragi ce ta kare daga Arsenal)

Gabriel Slonina (fam miliyan 12.3 daga Chicago Fire)

Carney Chukwuemeka (fam miliyan 20 daga Aston Villa)

Marc Cucurella (fam miliyan 55 daga Brighton)

'Yan wasan da suka bar Chelsea a bana

Antonio Rudiger

Asalin hoton, Getty Images

Antonio Rudiger (Kwantiragi ya kare ya koma Real Madrid)

Charly Musonda (zamansa ya kare a kungiyar )

Danny Drinkwater (zamansa ya kare a kungiyar)

Jake Clarke-Salter (Kwantiragi ya kare ya koma Queens Park Rangers)

Andreas Christensen (Kwantiragi ya kare ya koma Barcelona)

Matt Miazga (Kwantiragi ya kare ya koma FC Cincinnati)

Timo Werner (An sayar da shi fam miliyan 18 ga RB Leipzig)

Wadanda ta bayar aro a kakar nan

Romelu Lukaku

Asalin hoton, Getty Images

Romelu Lukaku (Inter Milan)

Lucas Bergstrom (Mai tsaron raga zuwa Peterborough

Jamie Cumming (Mai tsaron raga zuwa MK Dons

Nathan Baxter (Mai tsaron raga zuwa Hull

Henry Lawrence zuwa MK Dons

Malang Sarr zuwa Monaco

Ian Maatsen zuwa Burnley

Faustino Anjorin zuwa Huddersfield

Sam McClelland zuwa Barrow

Levi Colwill (Brighton & Hove Albion)

Leeds United vs Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A kakar da ta wuce Chelsea ba ta dauki kofi ko daya ba, sannan ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Liverpool a FA Cup da kuma League Cup.

Kawo yanzu attajiran da suka sayi Chelsea na fatan za ta yi abin azo a gani a kakar nan, wadanda suka bude bakin aljihu don dauko duk dan wasan da Tuchel ke bukata.

Saboda haka tun yanzu kociyan dan kasar Jamus sai ya kara sa kwazo idan ba haka ba ya fara fuskantar kalubale.

Koda yake mahukuntan Chelsea sun fara tattaunawa da Tuchel domin a tsawaita yarjejeniyarsa, domin ya ci gaba da jan ragamar kungiyar.

Tuchel ya karbi jan kati a wasa da Tottenham a Stamford Bridge, zai yi hutun wasa daya, amma ssai hukumar kwallon kafar Ingila ta kammala bincike.

An kuma ci tarar kociyan da na Tottenham Antonio Conte kan halayyar da suka nuna ta tayar da yamutsi.

Ranar Asabar 27 ga watan Agusta Chelsea za ta karbi bakuncin Leicester City a wasan mako na hudu a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Wasannin da ke gaban Chelsea a gasar Premier League

Premier League ranar Talata 30 ga watan Agusta     

Southampton da Chelsea       

Premier League ranar 4 ga watan Satumba   

Chelsea da West Ham

Premier League ranar Asabar 10 ga watan Satumba 

Fulham da Chelsea     

Premier League ranar Lahadi 18 ga watan Satumba 

Chelsea da Liverpool 

Premier League Asabar 1 ga watan Satumba

Crystal Palace da Chelsea