‘Ku karbi kudi idan an ba ku a lokacin zabe amma ku zabi cancanta’

Kudi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Yayin da babban zabe a Najeriya ke tafe, wasu ‘yan siyasa a kasar sun ce ba laifi bane masu kada kuri’a su karbi kudi idan an basu a lokacin zabe, amma kuma su zabi cancanta.

 ‘Yan siyasar sun bayyana hakan ne a yayin da wasu masana da kungiyoyin kare dimokradiyya ke fargabar cewar siyasar kudi musamman sayen kuri’u na iya mamaye babban zaben kasar da ke tafe.

 Hon Yusuf Umar Garkuwa, matashin ɗan siyasa ne daga jihar Kaduna, ya shaida wa BBC cewa, ba bu laifi masu zaɓe su karɓi kuɗi, tun da ko sun karɓa ba wanda zai tilasta musu zaɓen wanda ba sa ra'ayi.

 Ya ce ya na ganin hakan zai magance matsalar siyasar kuɗi gaba ɗaya a Najeriya.

 Hon Yusuf Umar Garkuwa, ya ce “ Shi zabe abu ne da za ayi shi a boye, don haka don mutum ya baka kudi ka zabe shi bai isa ya bika akwatin zabe don ganin abin da zaka zaba ba.”

 

Saboda haka ka amshi kudin, amma kuma ka zabi abin da ya dace in ji shi.

 Ya ce idan har ‘yan siyasa na bayar da kudi ana karba kuma ba a zabensu, ai gobe ba zaka fito ka kara bayar da kudi don a zabe ka ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

 Kuma idan ma ka ga wani zai bayar da kudi don a zabe shi ai zaka bashi shawara a kan kada ya soma don kai ma kayi baka ji dadi ba in ji shi.

 Hon Yusuf Umar Garkuwa, ya ce idan har ana yin haka to a iya samun sauki a siyasar kudin da ake a Najeriya.

 Matashin dan siyasar ya ce, ‘‘Idan har ana wayar wa mutane kai a kan ‘yancinsu, da kuma zabar cancanta, za a rinka samun sauki a siyasar kudi, domin mutane za su karbi kudin dan takara amma kuma su zabi abin da suke so.”

 Ya ce ba wai siyasar kudi ba zata yi tasiri a zaben mai zuwa ba, zata yi a wasu wuraren, amma ba a ko ina ba, don haka in da zata yi tasirin ma yakamata mutane su gane ‘yancinsu na shekara hudu suke sayarwa.

 Hon Yusuf Umar Garkuwa, ya ce akwai wasu ‘yan takarar da basu da abin da zasu fada a zabe su ko kuma su nuna, don haka dole su fito da kudi a lokacin zabe saboda akwai talauci da yunwa da ke addabar mutane.

Ya ce don haka ku karba ku cinye ku zabi wanda kuke ganin ya fi cancanta.