Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Richarlison zai nemi shawarar ƙwararru
Dan wasan Tottenham, Richarlison ya ce zai nemi shawarar ƙwararru, idan ya koma Ingila, bayan ya je buga wa Brazil tamaula.
An nuna Richarlison na sharɓar kuka, bayan an sauya shi a wasan da Brazil ta doke Bolivia 5-1 ranar Asabar.
Ɗan wasan ya ci ƙwallo huɗu a karawa 40 a Tottenham, bayan ya koma kulob ɗin daga Everton a bara kan kuɗi fam miliyan 60.
''Ina cikin wani yanayi na damuwa a rayuwa kusan wata biyar, kamar yadda ya sanar da wata kafar yaɗa labarai a Brazil, O Globo.
''Yanzu abubuwa sun fara komawa yadda ya kamata a gida. Mutannen da suka sa ido kan kuɗin da nake da shi, yanzu ba sa kusa da ni.
''Abubuwa za su koma kamar yadda aka saba, ina da tabbaci zan koma kan ganiya a Tottenham.
''Zan nemi shawarar ƙwararru da zarar na koma Ingila, domin a ƙara min ƙwarin gwiwa, hakan ne zai taimaka min ƙara sa kwazo a tamaula.''
Richarlison ya ɓarar da damarmaki kafin daga baya Brazil ta canza shi a minti na 71, a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Bolivia.
Haka kuma an sauya shi a minti na 64 ranar Talata a karawar da Brazil ta ci Peru 1-0 a Lima yayin wasan shiga babbar gasar ƙwallon ƙafa ta duniya.
O Globo ta ruwaito cewar Richarlison ya raba gari da mai kula da harkokin ƙwallonsa, Renato Velasco.
Brazil za ta ci gaba da buga wasannin neman gurbin zuwa gasar kofin duniya ranar 13 ga watan Oktoba da Venezuela, sannan ta kece-raini da Uruguay kwana uku tsakani.
Tottenham, wadda take ta biyu a teburin Premier League za ta karɓi baƙuncin Sheffield United ranar Asabar a karawar mako na biyar.