Fitaccen ɗan ƙwallon duniya Pele ya rasu

Pele

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Fitaccen ɗan ƙwallon nan na duniya ɗan ƙsar Brazil, Pele ya rasu yana da shekara 82.

Pele ya rasu ne a ranar Alhamis 29 ga watan Disamban 2022 bayan ya sha fama da rashin lafiya.

A kwanakin baya an yi ta yaɗa labarin ƙarya na rasuwarsa.

Ya rasu ne sakamakon cutar kansar ƙaba da kuma cutar ƙoda

Ana ganin Pele shi ne ɗan ƙwallon da ba a taɓa samun irin sa ba a duniya, kuma sau uku yana cin gasar kofin duniya wa ƙasarsa Brazil.

Ya ci kofin duniya a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1970.

A shekarar 2000 ne kuma hukumar ƙwallon ƙafar duniya FIFA, ta ayyana shi a matsayin ɗan ƙwallon ƙarni.

Shi ne ɗan ƙwallon da ya kafa tarihin zura ƙwallaye 1,281 a raga a cikin wasanni 1,363 cikin shekara 21 da ya yi yana buga tamaula.

Cikin waɗannan har da ƙwallo 77 da ya ci wa ƙasarsa cikin wasanni 92 da ya buga wa Brazil ɗin.

An yi wa Pele tiyata a kan yanke masa kansa a hanjinsa a watan Satumban 2021 a Asibitin Albert Einstein da ke Sao Paulo.

An sake kwantar da shi a asibiti a watan Nuwamban 2022.

Ƴarsa Kely Nascimento ta yi ta sanar da masoya halin da mahaifinta ke ciki a shafukan sada zumunta daga asibitin da yake jinya.

A ranar Alhamis ɗin ta wallafa wani hoto da ke nuna hannayen iyalan Pelen a kan jikinsa a asibiti inda ta rubuta: "Muna maka godiya kan duk abin da ka yi mana. Muna matuƙar ƙaunarka. Allah Ya ji ƙanka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Fitattun 'yan ƙwallon ƙafa na duniya da shugabanni a harkar ne ke ci gaba da miƙa saƙon ta'aziyya kan rasuwar Pele - wanda a iya cewa shi ne ɗan ƙwallon ƙafan da babu kamarsa a duniya - bayan ya mutu yana da shekara 82.

A mahaifarsa Brazil, ana ɗaukarsa a matsayin wata kadarar ƙasar, kuma gwarzo.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Luiz Inacio Lula da Silva ya ce ba a taɓa yin ɗan ball kamar Pele ba.

Cikin masu nuna alhinin mutuwar Pele, akwai shugaban Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA, Gianni Infantino, wanda a wani saƙon bidiyo da ya wallafa a Instagram ya ce ga masu sha'awar ƙwallon ƙafa, lallai wannan rana ce da ba a fatan zuwanta.

An rasa Pele, an rasa Sarki, in ji shi.

Shi ma babban tauraron ƙwallon ƙafa na Brazil a yanzu Neymar ya ce Pele ya zama murya ga talakawa da mutane baƙaƙen fata da kuma musamman ya fito da Brazil.

Yayin da babban tauraron ƙwallon ƙafa na Faransa Kylian Mbappe ya ce gadon da Pele ya bari, ba za a taɓa mantawa da shi ba.

Eduardo Goncalves de Andrade wanda aka fi sani da Tostao tsohon ɗan ƙwallon Brazil ne kuma ya yi wasa da Pele: "Yau rana ce ta baƙin ciki. Pele mutum ne da ya haɗa nagartar zama hamshaƙin tauraro mafi ɗaukaka.

Idan an bar fili, a ko da yaushe cike yake da murmushi, mutum ne mai son kula da kowa. Wata ɗaukaka ce gare ni da na buga ƙwallo da Pele. Yayin wata hira da BBC a 2006, an tambayi marigayi Pele ko yana jin cewa shi ne ɗan ƙwallon da ya fi shahara?

Ba na jin haka, na tabbata, in ji Pele. Ba kowa ne yake son Pele ba, na tabbata.

Pele dai gwarzo ne a Brazil, da ya ci wa ƙasar kofin duniya har sau uku. Matashi ne haziƙi da ya fara ƙwallo ajin ƙwararru a ƙungiyar Santos yana ɗan shekara 15.

Ƙasa da shekara biyu bayan nan, ya ba da gagarumar gudunmawa ga nasarar Brazil wajen cin Kofin Duniya bayan lallasa Sweden.

A tsawon shekara 20 da ya yi yana buga ƙwallon ƙafa, Pele ya ci ƙwallo fiye da dubu.

Ana kallon Pele, wanda sunansa na ainihi Edson Arantes do Nascimento a matsayin jakadan Brazil mafi shahara da aka taɓa yi.

Ga mutane da dama, Pele ya haɗa duk wani alheri da ƙasar ke taƙama da shi ta hanyar kirkinsa da baiwar ƙirƙira da kuma nasara.