Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Malam Ya’u Hussaini Dodo
A wannan mako, shirin Ku San Malamanku ya tattauna da malamin addinin Musulunci Malam Ya’u Hussaini Dodo.
An haifi malamin ne a anguwar Sharifai da ke birnin Kano.
Ya taso ne a Dorayi, a gidan malam Mamman mai ‘yan makaranta wanda aka fi sani da Mai Mari.
A wurin ne ya yi karatun Al-Qur’ani har kuma ya sauke, inda daga baya ya tafi makarantar Firamare ta U.P.E Warure.
Ya kasance aji ɗaya da Malam Umar Sani Fagge da Tijjani Musa Rufai da sauransu.
Daga nan sai ya koma karantarwa a makarantar Festival a shekarar.
Daga baya, ya koma inda ya ci gaba da karatun sakandire a High Islamic da ke Hadejia.
Malamin ya kuma ce ya yi yawon yin wa’azi tare da Marigayi Malam Kamalu Adamu na Ma’aji wanda ya koya masa yin wa’azi.
Malam ya ce an fi yi masa tambayoyi ne kan matsalolin da suka shafi aure.
Saboda irin waɗannan matsaloli ne Malam ya rubuta litattafai kamar irin su Gishirin Ma'aurata da kuma wani littafi da ake kira Boka kake ko Malam.
Ya ce abin da ya fi faranta masa rai shi ne idan aka faɗa masa labarin kirkin Manzon Allah S.A.W.